Tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ibrahim Mantu ya kwanta dama

Allah Ya yi wa tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ibrahim Nasiru Mantu.

Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a cikin daren Litinin a wata asibitin Abuja bayan fama da rashin lafiya.

A halin rayuwarsa, marigayin cikakken ɗan siyasa ne, kuma tsohon sanata da ya wakilci Filato ta Tsakiya a Majalisar Dattawa. An zaɓe shi a matsayin sanata ne 1999 inda ya zama mataimakin shugaban Majalisar a shekarar 2000.

Baya ga haka, Mantu ya yi aiki a wurare da dama tare da riƙe muƙamai daban-daban inda ya ba da tasa gudunmawa ga cigaban ƙasa.

An haifi Mantu ne a ranar 16 ga Fabrairun 1947 a jihar Filato inda ya bar duniya yana da shekara 74.