
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce jam’iyyun adawa ba za su samu haɗin kan da suke nema ba matuƙar za su cigaba da sukar duk abinda ya shafi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyya mai mulki (APC).
Akpabio ya bayyana hakan ne a yayin taron ƙaddamar da wani sashi na titin jirgin ƙasa a Abuja. Taron ya samu halartar wasu jiga-jigan PDP da suka haɗa da tsofaffin gwamnonin jihohin Enugu da Ekiti, wato Ifeanyi Ugwanyi da Ayo Fayose.
Shugaban Majalisar Dattawan ya faɗi haka ne bisa la’akari da kalaman Tinubu na Ranar Dimukraɗiyya, na ƙaryata batun cewa APC tana shirin rushe jam’iyyun adawa da mayar da Nijeriya ƙasar jam’iyya ɗaya tilo, da cewa yana farin cikin ganin ƴan ɓangaren adawa a rabe.
A madadin haka, Akpabio ya ce, Shugaban ƙasar ya yi ikirarin cewa ba ya son ganin Nijeriya a matsayin ƙasa ta jam’iyya ɗaya, inda ya yi fatan a samu haɗin kai a tsakanin ɓangaren adawa.
Ya ce, Tinubu ya faɗi haka ne domin kada a samu hujjar cewa yana yunƙurin rufe bakin ƴan adawa da hana su tasiri a yayin babban zaɓen da ke tafe.
Duba da yadda ake samun ɓaraka a tsakanin ƴaƴan jam’iyyun PDP da LP da hakan ya kai wasu ga zuwa kotu, ya sanya ƴan siyasa mayar da APC jam’iyyar da ta fi dacewa ga harkokin siyasarsu musamman ganin yadda gwamnonin PDP biyu, wato Sheriff Oborevwori (Delta) da Umo Eno (Akwa-Ibom) suka sauya sheƙa zuwa APC a kwanakin baya.
Haka kuma wasu daga cikin ƴan PDP, LP da APC sun fice zuwa jam’iyyar SDP a yunƙurin ƴan siyasa na samar da haɗaka da za ta kawar da mulkin APC a 2027.
