Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Har Shehu Usmanu Danfodiyo ya koma ga Allah a shekaru 63 bai samu zarafin yin hajji ba don sadaukar da kansa kakaf ga koyarwa. Kama daga ƙofar gidansa, masallaci har duk inda ya nufa a cikin jama’arsa. Hatta kaninsa Sheikh Abdullahi Gwandu ya yi yunƙurin tafiya aikin hajji amma kanawa su ka dakatar da shi don ya koya mu su addini.
Gaba ɗaya rayuwar Shehu Mujaddadi a hidimar karatu, karantarwa da wayar da kan al’umma ne kan dokokin addinin Musulunci na ƙarfafa gaskiya da amana da tarbiyya. Wannan ya sa ba a samun ko rabin sa’a a wuni ta yin wasu hidimomi na daban balle kama hanya da kafa don tafiya aikin hajji. Ba kamar yadda a zamanin yau cikin sa’a 4 daga Sokoto maniyyaci zai hau jirgi fir ya sauka a kasa mai tsarki ba, a zamanin Shehu zamani ne guda na shekaru a ke ɗauka a hanya a ratsa Sahara ko a samu aikin hajjin ko a rasa rai ko ma wasu su zauna kan hanya wajen cin zango a Chadi ko Sudan.
Hatta ƙanin Shehu Mujaddadi wato Balaraben Biladis Sudan Sheikh Abdullahi Gwandu bai samu yin aikin hajji ba duk da ya shirya tafiya ya iso Kano don wucewa amma ɗaliban ilimi su ka dakatar da shi don ya koya mu su karatu. Haka kuwa a ka yi ya sarayar da tafiyar ya tsaya ya koyar har ma ya wallafa littafi da har yanzu a ke cin gajiya. Bayan nan haka ya juyo gida don damar ba ta samu ba.
Gaba ɗaya tafiya rangaɗi ko ƙele-ƙelen duniyan nan ba sa gaban Shehu don aikin da ke ma sa daɗi shi ne ya ga ya koyawa jama’arsa tauhidi su tsira daga nau’o’in shirka da camfe-camfe na bautar Aljana Doguwa da ƙananan alloli gizagizai.
Ko yau a sabon zamanin nan bayan fiye da shekara 200, in mutum ya ziyarci gidan Shehu zai gane tsangaya ce kawai ta koyar da karatu don ba wani abu na zamani ko more rayuwar duniya. Mai zurfin imani ma wajen sanin gwagwarmayar Shehu sai ya zubar da hawaye in ya shiga gidan mai albarka. Duk zargin wasu na maida wajen yin bidi’o’i ko ma neman tubarraki, ya saɓa da koyarwar Shehu kuma ya rubuta hakan ƙarara a littattafansa. Shehu ya rubuta littafin IHYA’US SUNNAH don yin rugu-rugu ga bidi’a da duk dangoginta. Haba ai mu da Shehu sai addu’ar rahama da shi sam barka ga rayuwa abar koyi. Ka zaga ta bayan dakin Shehu ka ga kabarin Nana Asmau! Wai ai nan za ka san Allah ya tara manya a zamanin nan na Shehu maza da mata da su ka yi hidima ga tauhidi har su ka koma ga Allah.
Shehu bai bar zinari ko azurfa ba amma ya gadar da ilimi kuma ya samu lokaci ya rubuta duk saƙonnin a littattafai kamar yadda dan uwansa Sheikh Gwandu shi ma ya yi hakan. Allahu Akbar.
Turawa sun yaƙi daular shehu, sun kashe jama’ar shehu amma sun gaza murƙushe addinin shehu! wallahi da Shehu sarauta ya kafa da tarihinsa ya gushe amma ilimi da tauhidi ya yada.
Cikin farin ciki har yau bayan fiye da shekaru 200 da rasuwar Shehu Usman Mujaddadi, idan masoya ko makiya na magana a kan sa, sai ka ɗauka ya na nan ma a raye. Yadda a ke ambatar sunansa kullum ya nuna muhimmancinsa duk da iya ƙoƙari da dukkan makirci da Turawa su ka yi na rufe babinsa ta hanyar bi garuruwan Daular Sokoto su na buɗe wuta da manyan bindigogi su na kisan gilla ga jama’ar Shehu. Sun kona na konawa, sun sa wasu tafiya hijira da har yau ɗin nan zuriyarsu ba ta dawo nan Arewa ba.
Sarautar da a ke yi tun 1903, ta fara ne daga tsarin da Turawa su ka kawo kuma ba tare da kowa na ɗaukar umurni daga Sakkwato ba. Hatta sunan AMIRAL MUMUNIN sun canja shi zuwa lakabin SULTAN yayin da sarakunan Musulunci na Daular su ka maida su na gargajiya. Ba nan Yammawa su ka tsaya ba, sun cigaba da yada addininsu ga wasu sassa na ciki da gefen Daular da su ka rusa. Sun yi amfani da baƙaƙen fata daga waɗanda su ka ribata su ka ɗinka mu su gajerun wanduna da lasar takobi a rantsuwa maimakon Allah, su ka damka mu su makamai don su kashe duk wanda ke mubaya’a ga tauhidin da Shehu ya ƙarfafa.
Wallahi cikin masu adawa da Shehu a zamanin nan har da jikan ɗaya daga sojojin da su ka yaƙi Daular Sakkwato.
Akwai wani madugu daga masu ruruta fitinar kiyayya ga Shehu a nan Arewa mai matsayin Farfesa wanda asalin kakanninsa, na cikin rundunar Turawa da a ka yi amfani da su wajen bin gari-gari don kawar da Daular Sakkwato da kashe duk wanda su ka samu ya na biyayya ga tauhidi. Wannan mamuguncin mutumin na kwana ya wuni ya na kulle-kullen hanyoyin da zai yaki musulunci da haddasa fitina a Arewa don karisa makircin da iyayensa bayin Turawa su ka fara amma su ka gaza cimma buri. In Allah ya yarda zan fito da ƙarin bayani kan wannan bayan kammala jerin rubutu 10 da na ke kai a yanzu.
Duk waɗannan kashe-kashe da shigo da barasa irin ta Yammawa da tsari na fasikanci da jajayen kunne su ka gabatar ga al’ummar Daula ya ci nasarar zahiri, amma abu daya da har kiyama ta tsaya ba za su iya markaɗewa ba shi ne TAUHIDI- KALIMATULLAHI HIYAL ULYA ko ba sa so sai an yi kiran sallah sau 5 a wuni a tsohuwar Daular Sakkwato; su toshe kunne ko su buɗe SAMMAKAL.
Zallawa na cewa da ba Shehu, da arewa ta na gogayya da Turai, alhali a Kamaru inda ba Shehu sai su Ouba Ali Mohaman, sabulu ba riga su ke kerawa! sai da Shehu ya yi shekara 116 da rasuwa gabanin haihuwar Ojukwu balle kanu mai Aifob.
Gaskiyar magana in ka ga mutane sun taru don adawa da wani wanda Allah ya yiwa rasuwa a wani ƙarni ma daban da karninsu, to ya kafa wani abu ne mai tasirin da ke hana muradunsu rawar gaban hantsi. Shehu Mujaddadi ba masarautu ya kafa ba sam amma ya ƙarfafa malamai don su yi ta koyar da darusan Islama a birane da karkara da bai taɓa taka wajajen da kafarsa ba. Idan wani ya ce Shehu ya kafa sarautu, to Turawa sun zo sun kashe duk wanda su ka ga zai mu su tarnaki sun kawar da Daular tun 1903 sun kafa tsarinsu da yayata addininsu da hayaƙin tabarsu da giyarsu ta zamani. Wallahi masu kwangilar yaƙi da Shehu na yaki ne da addinin Musulunci da Shehu ya ƙarfafa, ba da barin damar annanci da shaidanci ba. Duk mai fada da tauhidi ya shafawa kansa ruwa a zamanin Shehu don tasirin tsoron Allah da zama ƙarƙashin gwamnati mai gaskiya da amana. Shi addinin Musulunci na da tsari na kulawa da haƙƙoƙin jama’a da hana zaluntar kowa. Ba ma buƙatar a faɗawa mutum ya bi doka don gani ga wane ua ishi wane tsoron Allah. Ma’ana a duk inda a ke aiki da dokokin Allah to mutane za su sauya su zama na kirki ba cuta ba cutarwa.
Ba kamar yadda Turawa su ka ci nsarar canja ɗabi’un mutanen kasashen Afurka da ba su da ruhi irin na Mujaddadi ba, a nan Arewa sun cika da mamakin rayuwa da mutane masu tsarin shugabanci da tarbiyyar addini ta sai Mahadi-ka-ture. Duk mai inkari ya zaga wasu kasashen Afurka ya ga yadda mutanen ke ƙoƙarin zama baƙaƙen Turawa abun tausayi baubayin bayi marar sa alƙibla don rashin ruhin tauhidi.
Ba ma wasu ƙasashe ba, mutum ya shiga yankunan kudu inda ba yankin Daular Sakkwato ba ya ga rayuwar mutane da su ke ɗaukar Bature a matsayin wani mala’ika don haka za ka ga tikekiyar mata da dan kamfai an kona gashi a na tafiya tamkar ta zamanin jahiliyya. Dattijo dan 80 ya murɗe wuya da nektayin ya zura kai cike da furfura cikin malafa kamar mai tallata tabar malboro. Allah mun gode ma ka da kyautar Shehu Mujaddadi a Nijeriya, Malam na kwance a kabarinsa wasu na kwana su wuni a soshiyal midiya wai su na yaƙi da shi! sakarkaru karnukan farautar ALLAZINA KAFARU.
KAMMALAWA
Na ga wasu tsageru na cewa da Shehu bai kare kansa ba, da yau Arewa na gogayya da ƙasashen Turai wajen kere-kere da cigaban zamani. In haka ne yaya a ka yi Kamaru da ba irin Mujaddadi sai su Ouba Ali Mohaman ba su kera jiragen sama ba sai wani katon sabulu ba riga ɗan Kamaru?. Kai su tambayi mutan Ingila su mu su bitar tarihi, duk kwarewar Bature/Turawa karkashin Gwamna Lugga sai da su ka yi turus da sallamawa tsarin gwamnatin Shehu kuma har su ka koyi wasu sabbin dabarun rayuwa da har gobe na amfanar su wajen jagoranci na gaskiya da amana da ware mafi yawan lokaci kan ilimi da ilmantarwa.
Haƙiƙa duk mai tunanin zai iya kawar da koyarwar tauhidi ta Shehu, ya sake dabara don wannan tsari zai zauna daram ila yaumil ƙiyamati.
