Rarara annoba ne ga Kano da Arewa?

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

A baya, ban taba bata lokaci don yin rubutu game da Rarara ba, amma a wannan lokaci ya zama wajibi ga duk mai kishin Arewa da Musulmi ya yi Allah wadai da irin halayya da wakokin Rarara.

Komai kiyayyarka da Rarara dole ka sallama wajen yarda da cewa hakika Allah ya ba shi ni’ima ta basirar waka. Ita kuma waka, ko su mawaka, Allah ya sanar da mu cikin suratul Shu’ara cewa kashi biyu ne:

Q22:226 “Kuma mawãƙa, halakakku ne ke bin su. Shin, ba ku ga cewa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙetare haddi) ba? Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa? Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa.”

To akasarin mawaka zaka samu masu batanci, badala, banbadanci, zage-zage, zambo da kawo rarrabuwa cikin jama’a da sauransu, shi kawai su ka sa a gaba. Kuma yawancin wadanda za su bi su zaka samu mutane ne wadanda basu da daraja, marasa kunya, kaskantattu ke biye musu. Sai kuma wasu kalilan na mawakan wadanda masu tsoron Allah ne da ambatonsa, da kare masu rauni da yada abubuwa na alheri. 
A satin nan, wani taro na masana da aka aiwatar a jihar Katsina game da fitattun mawaka biyu, wato Mamman Shata da Kahutu Rarara, hakika duk wanda ya halarta ko ya Kalli Shirin, da ake neman gwada tsakanin Shata da Rarara, zai yaba yadda, musamman hujjojin Prof Aliyu Kankara, inda suka nuna cewar banbancin Shata da Rarara, tamkar na tsakanin Al’arshi ne da Duniya. 

Ku kanku masu karatu, idan kuka dauko waccan Aya ta suratul Shu’ara, hakika zaku saka Rarara a jerin na farko da Allah ya fada, sannan ku saka Shata a Jeri na biyu. Domin Shata dai yayi wakoki sama da dubu goma, amma Rarara ko Dari biyu bai yi ba zuwa yanzu. Sannan wakokin Shata babu wani bigire na rayuwa, kama daga tarbiya, hadin Kai, Imani, addini, makwabtaka, Ilimi, wayar da Kai dss da bai yi ba. Amma na Rarara kaf babu komai cikinsu sai zagi da cin mutunci, assasa tumasanci, habaka raini, kawo rarrabuwar mutane, da daurewa zalunci gindi da sauransu.

Rarara, ya bada babbar gudunmuwa wajen bata tarbiyar matasa, musamman a siyasance. A nan Jihar Kano ya bi Kwankwaso, ya dawo ya zage shi, ya bi Ganduje, ya dawo ya zage shi, haka ma Abba. Idan akwai wani wanda ta silarsa Rarara ya sami daukaka a kasar nan, Buhari ne da gwamnatinsa, amma saboda haramci irin na Rarara sai da ya dawo ya zagi Buhari. Babu wani mahaluki yau a Arewa da zaka ce ya ci fassarar zancen bahaushe da ke cewa ‘Bakin-ganga” irin Rarara. Ya zama Karen farautar gurbatattun Yan siyasa da masu mulki.

Hatta wadanda ba musulmi ba, mutane masu hankali da daraja irinsu… na ga ya yi kakkausar suka ga sabuwar wakar da Rararan yayi wa Pantami. Amma fa kada mu dora wa Rarara laifi kacokan, domin sai bango ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga. Sannan ita annoba, ko ambaliya ta wani mugun aiki, tare ta ake yi kafin ta barke, domin da zarar ta barko, zata yi ambaliya ne da kowa. A lokacin da Buhari da APC ke cin karen su babu babbaka, Rarara ya yi iya shegensa son rasa, har sunan banza na ‘Tsula” ya sakawa Kwankwaso, a wancan lokacin, ludayin su Pantami na kan dawo, amma ba su yi wani kokari, a matsayinsu na shugabannin siyasa da malanta wajen takawa Rarara burki ba, yau ga shi ambaliyar fitsarar Rararan ta mamayi Pantami. Don haka wajibi ne mutane masu hankali a Kano da Arewa su tashi su takawa Rarara burki.

Waƙoƙinsa kaf sun fada a fagen jerin wadanda Allah da kansa ya gargade mu akai, wato wakokin da suke daure gindin barayin ya siyasa, da nuna cewa shugabanni su yi abinda su ka dama, duk da sun kasa gyara tsari a yabi cewa sun yi, a wulakanta da cin mutunci duk wanda ba ya APC, a ci gaba da maida Yan Arewa almajirai ana raba musu shinkafa. Mu dubu yadda a masana’antar Kannywood ta zama ana banbadanci saboda yar tsaba da za’a ba mutane. Duk ta dalilin Rarara.

Wallahi ko kasashe irinsu Amurka Yan badala, akwai yanayin da mawaki, idan rashin kunyarsa da lalata al’ada zai wuce gona da iri, ake taka masa burki. Misali a shekarar 1990 an hana wakokin 2live Crew. Kasar Malaysia ta hana Beyonce wasa a kasarta saboda shigar tsiraici. BBC da gidajen Radio a Amurka sun hana wakar George Micheal. China sun hana Lady Gaga da Justin Bieber wasa a kasarsu. Don Allah idan wadanda ba musulmi ba na kokarin ganin cewa mawaka su na kasancewar masu tsaftar kalamai da shiga, ina ga wadanda ke tunkahon Shari’ar musulunci, Yan Hisba da Cencor board?

Wajibi a takawa Rarara burki a wannan yanki, manyanmu da yaranmu, Maza da mata, mu fito ta hanyar social media mu yaki wannan mummunar al’ada sannan manyan, su dauki darasin abinda ya faru da Pantami, a dauki mataki tun da wuri. A karshe kuma na kalubalanci kowa, a kan ko akwai wanda zai iya dauke Rarara daga jerin miyagun mawaka da suratul Shu’ara ta banbance shi, ya dawo da shi jerin su Shata?

By ukarofi

Leave a Reply