Nazari kan matsalolin noma a daminar bana

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Wani rahoto da jaridar Manhaja Blueprint ta wallafa game da matsalolin da manoma ke fuskanta a daminar bana, dangane da ƙalubalen noma da tsadar abinci ya ja hankalina sosai, musamman ganin cewa jama’a da dama na sa ran ganin an samu sauƙin farashin kayan abinci a kasuwanni, saboda yanayin da ake ciki na damina, yayin da manoma a wasu sassan arewacin ƙasar nan suka fara fitar da kayan gona zuwa kasuwanni. 

Rahoton ya naaalto Babban Sakataren ƙungiyar Manoma ta ƙasa (AFAN), Femi Oke, yana bayyana cewa, har kawo yanzu ana cigaba da samun hauhawar farashin kayayyakin amfanin gona saboda matsalolin da manoma ke fuskanta, duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na samar da yanayi mai kyau ga manoma.

Ya ce, matuƙar manoma ba su samu cikakken tsaro ba a gonakin su ba, da wuya su samu sakewar da za su noma isasshen amfanin da zai wadata a kasuwanni har a samu raguwar farashin kayan abinci. Kodayake, ko a yanzu ma tsadar ba ta yi yawa sosai ba, amma ba za a ce sambarka ba.

Iyalai da dama na fuskantar ƙarancin abinci da rashin samun abinci mai gina jiki, sakamakon tsadar abinci da lalacewar tattalin arziki. Yin abinci da nama, ko karyawa da shayi da madara da ƙwai ya zama tarihi a wasu gidajen, wasu kuma sai jifa-jifa, saboda yanayin da ake ciki. Cin abinci sau uku a rana yana gagarar iyalai da dama.

Wannan yana sa rayuwa tana ƙara zama cikin ƙunci da rashin walwala, ƙwazon yara a makaranta yana raguwa sosai saboda rashin abinci mai gina jiki. Wasu yara da yunwa suke zuwa makaranta, ko dai ba su samu abinci sun ci ba, ko kuma wanda suka ci bai ishe su ba. Su kansu iyayen da ke fita suna nema ba sa samun abincin su ci a wadace. A gida ba su samu sun ci isasshe ba, a waje kuma tsadarsa ta sa ba sa iya rufe ido su saya.

A rahoton da Hukumar Kula da Abinci ta Duniya ta fitar cikin watan Afrilu da ya gabata an bayyana sunan Nijeriya a cikin jerin ƙasashen da ke fama da matsalar ƙarancin abinci da tsadar kayan amfanin gona, wanda shi ma rahoton ya danganta da ƙaruwar ayyukan ta’addanci a ƙauyuka inda ake da manyan gonaki kuma ake noman kayan abinci sosai. Garkuwa da manoma ko sanya musu harajin miliyoyin kuɗi kafin su yi noma a gonakinsu, ya sa da dama sun haƙura da yin noman sun koma wasu sana’o’in, ko ma dai sun yi hijira sun bar wuraren su na asali.

Rahoton da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar a watan Yuni na 2026 game da hauhawar farashin kayayyaki ya nuna lallai akwai abin nuna damuwa a kan yiwuwar samun yunwa a wasu sassan arewacin ƙasar nan, inda ayyukan ta’addanci ya fi tsamari. Hatta a jihohin Arewa ta Tsakiya, inda nan ma matsalar tsaron take gajiyar da manoman yankin da rikice-rikicen ƙabilanci, noma ya ja baya sosai.

Babban Sakataren ƙungiyar Manoma ta ƙasa Femi Oke ya kuma danganta tashin farashin kayan abinci da mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa da suka lalata gonaki a wasu sassan ƙasar nan, lamarin da ya rage yawan amfanin gona da ke shiga kasuwanni.

Duk da sabbin dabarun ayyukan noman zamani da ake ɓullo da su amfanin gonar da ake samu a Nijeriya a baya-bayan nan, mutane da yawa suna fuskantar haƙiƙanin gaskiya game da tashin farashin kayayyakin abinci a kasuwannin ƙasar nan. Wannan rashin daidaito yana haifar da tambayoyi game da abubuwan da ke shafar farashin abinci da tasirin su ga masu amfani da sauran ayyukan gona.

Manoman Nijeriya sun shahara a duniya ba ma a Afirka kaɗai ba, wajen fitar da amfanin gona masu yawa, irin su shinkafa, wake, masara, doya, dankali, rogo da sauran su. Kowacce shekara, manoma daga ko ina a faɗin ƙasar nan, amma halin tsaron da ƙasar nan ke ciki a halin yanzu ya canza wannan tarihin.

Daga cikin muhimman abubuwan da ke haifar da ƙaruwar farashin abinci a Nijeriya kamar yadda masana ke bayyanawa sun haɗa da matsalolin tattalin arziki da tsadar rayuwa, Duk da kasancewar yawan amfanin gonar da ake samar wa na iya ƙaruwa, farashin taki da sauran kayan noman, sufuri, da isar da kayan gona kasuwa da sayarwa ga jama’a yana ci gaba da tashi.

Sannan harwayau, akwai buƙatar gwamnati ta ƙara mayar da hankali ga gyaran hanyoyi, musamman hanyoyin karkara da na ƙananan hukumomi, saboda su ma na daga cikin matsalolin da ke addabar safarar kayan amfanin gona zuwa kasuwanni. Hakan na daga cikin dalilan da ke haifar da ƙarin kuɗin sufuri, wanda manoman da dillalai ke fakewa da shi suna ƙara farashin kayayyaki, wanda ke haddasa tsadar farashin kayan abinci ga masu saye.

Yadda dillalai a manyan kasuwannin kayan abinci ke tsawwala farashi, yadda ransu yake so, yana ƙara faɗaɗa yawan matsalar tsadar abinci da ake kuka da ita. Yadda ake takura wa ƙananan ’yan kasuwa yayin da ake ba su sarin kaya, saɓanin yadda su manoma suka ba da farashin sa a kasuwa, ya sa su ma suke huce haushin su akan ɗaiɗaikun mutane masu zuwa sayayya don kai wa gida wajen iyalansu.

A dalilin haka, iyalai da dama musamman masu ƙaramin ƙarfi da ke kashe mafi akasarin kuɗaɗen su a wajen cefanen kayan abinci. Tashin farashin kayan abinci na iya haifar da ƙaruwar ƙarancin abinci, inda ake tilasta wa iyalai yin zaɓi tsakanin biyan buƙatun yau da gobe na gida da suka zama dole kamar kiwon lafiya, ilimi, da abinci mai gina jiki.

Duk da ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya da masu ruwa da tsaki a harkar noma da samar da abinci ke cewa suna yi don ganin an magance wannan matsala ta tashin farashin kayan abinci, har yanzudai aljihun talaka bai shaida ba. Akwai buƙatar samar da wasu sabbin dabaru na inganta samar da abinci da sauƙaƙa farashinsa a kasuwanni, ƙara yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashe wa wajen tallafawa ayyukan gona. Samar da ingantattun hanyoyin sufuri don sauƙaƙe jigilar kayayyakin gona, da aiwatar da matakan sarrafa farashi don daidaita kasuwanni. 

Haka nan, akwai buƙatar gwamnati ta ƙara ƙoƙari wajen samar da ƙananan jari da basussukan da babu ruwa domin matasa su rungumi noman zamani, ta yadda sabbin dabarun da kimiyya da fasahohin noma suka kawo za a iya cin moriyar su. Sannan kuma gwamnati ta ƙarfafa samar da abinci na gida da rage dogaro da shigo da abinci daga waje, kamar yadda a baya gwamnati ta riƙa ba da tallafi ga masu noman shinkafa, alkama, da rogo. Hakan na iya taimakawa wajen wadatar abinci a kasuwannin cikin gida, rage farashin kayan abinci daga canje-canjen farashi a kasuwanni.

By ukarofi

Leave a Reply