Lakurawa sun kashe soja da ‘yan sa kai biyu a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Dandi sun bayyana cewa wani soja da ‘yan sa kai biyu sun rasa ran su a wani artabu tsakanin su da lakurawa jiya a ƙauyen Tashar Jiba da ke kan hanyar Kamba zuwa Kangiwa.

Wani mazauni garin Kamba Malam Aliyu Ibrahim ya bayyana cewa bayan samun labarin lakurawa sun kai hari a ƙauyen ne sai sojojin da ‘yan sa kai da ke aiki a wannan yankin suka isa inda suka fafata da su wanda a nan ne aka ce an yi wa jami’an kwanton ɓauna aka harbe su. Ya ce duk da ya ke ba shi da tabbacin su wanene suka mutu saboda ana raɗe-raɗin cewa soja biyu ne da ɗan sa kai ɗaya ne ko kuma soja ɗaya ne amma dai ya ga gawarwaki uku da aka kawo a babbar asibitin garin Kamba inda likitoci suka tabbatar da mutuwar su.

Ya bayyana cewa wannan ne kawai ya bayyana amma lakurawa da masu garkuwa da mutane sun daɗe suna cin karen su ba babbaka a wannan yankin ta hanyar ko dai ɗauki dai-dai ko kuma kawo mummunan hari wanda ya yi sanadiyyar yanzu haka ƙauyuka da yawa sun watse mutane sun koma waɗansu manyan garuruwa da ke kusa da su.

Wakilin mu ya nemi jin ta bakin rundunar yan sandan jihar Kebbi sai dai jami’in hulɗa da jama’a sufirtandan ‘yan sanda Bashir bai ɗauki waya ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton babu wani bayani daga rundunar yan sandan jihar ko kuma wata hukumar tsaro.

By ukarofi

Leave a Reply