Abu ne mai muhimmanci haɗa kai domin bunƙasa cigaban al’ummar Rano – Sarkin Rano

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Mai martaba Sarkin Rano Alhaji Muhammad Isah Umaru ya yi kira ga ‘yan asalin ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure akan su cigaba da haɗa kansu da tafiya tare domin  bunƙasa cigaban al’ummar yankin.

Ya bayyana haka ne a yayin taron karrama ‘yan asalin Rano dake ayyuka daban-daban a faɗin  ƙasar nan da aka yi a garin Rano  ranar Asabar.

Ya kuma ja hankalin mutanen da aka karrama su buɗe wata ƙungiya ta daban su haɗa kai da ƙungiyar RAKIBU da za su riƙa fito da al’amuran da zai taimaka ga cigaban al’ummar masarautar Rano.

Mai martaba Sarkin na Rano Alhaji Muhammad Isah Umaru ya bayyana mutuƙar jin daɗinsa da farin ciki da Allah ya azurta su da mutane masu kishi da kima da daraja da suke kula da cigaban yankin da kuma ɗaukaka kimarta a duniya. Ya yi fatan duk mutumin yankin da ya samu kansa a ko’ina zai zama jakada nagari ga yankin da kuma bada kulawa ga cigaban al’umma.

Da yake zantawa da yan jarida akan maƙasudin taron Umar Yunusa Rano da akafi sani da ɗanburan, shugaban gamayyar ƙungiyar  cigaban Rano,Kibiya, Bunkure da akafi sani da (RAKIBU) Rano, Kibiya, Bunkure Deɓelopment Association” ya ce an samar da ƙungiyar ne tun a baya sakamakon raba ƙananan hukumomi da akayi bayan suna dunƙule a baya gaba ɗaya sai suka fahimci abin kamar zai kawo rabuwar kai alhali suna tare iyaye da kakanni komai tare suke  yi.

Don haka suka ga cigaba ba zai samu ba a ɗaiɗai ku sai an haɗu wannan yasa suka haɗu aka samar da ƙungiyar ta RAKIBU a shekarar 2009 kuma an samar da cigaba masu tarin yawa daga kafa ta, ta wannan alaƙar an jajirce wajen taimakawa  samar da hanyoyi wadatattu masu inganci da suka taso daga ƙarfi har zuwa garin Sumaila da Bebeji sannan an samar da tsayayyen wutar lantarki da samar da Asibitoci da makarantu daban daban da kyakkyawan mu’amala da dukkan shugabannin da suke yankin ana yin magana da murya ɗaya a faɗa aji.

Ya ce wannan taro na karramawa anyi shine don iya mutane da suka fito daga Rano da suka sami cigaba a fannoni daban daban amma an haɗu Rano, Kibiya, Bunkure  an gabatar gaba ɗaya kuma a ciki yan kowace jam’iyya sun zo anyi taro an haɗu  anyi shawarwari ba wani da yasa bambancin siyasa.

Ya ce a cikin waɗanda aka karrama ba a  kalli wani yana siyasa kaza ba , an duba cancanta da daidaito ne da irin gudunmawar da suka bayar na cigaban yanki da ake buƙata sunyi  ƙoƙarin kaucewa siyasa ta kowane siga a tsara taron karramawar.

Shugaban na RAKIBU ya ce an karrama mutane 19 ne kuma acikinsu akwai farfesoshi guda Bakwai da shugaban gidan Radiyo na jihar Kano Adamu Abubakar Rano wanda shine na farko da suka taɓa samu daga yankin ya sami muƙamin, sun karrama wacce ta soma samun Kwamishina ta farko daga mata a yankin Hajiya Aisha Lawan Saje da kuma manyan daraktoci a hukumomin Gwamnati na tarayya  da manyan yan sanda kuma wannan sun soma ne da kaso na farko nan gaba za a zaɓi wasu a karrama su.

Ya ƙara da cewa bayan haka  kamar yanda aka yi a Rano za kuma suje Kibiya irin waɗannan mutane da suke da su za su fito dasu suyi a can haka kuma za a yi a Bunkure saboda gaba ɗaya wannan shi yake nuna ana tare a dunƙule komai da komai tare ake yi gaba ɗaya.

Umar Yunusa Rano “ɗanburan”ya ce  cigaba baya zuwa  wajen mutane in suna  zaune sai ita al’umma ta jajirce ta miƙe ta  tashi tsaye  ta je ta  nemo abinda  zai  kawo musu cigaba ita  kuma ɓangaren gwamnati in aka yi duba da  uzururruka na yi mata yawa,zata ce za tayi aiki kaza da kaza amma abubuwa da suke tasowa yau da kullum sai aga aikin ma sai a manta dashi ba a zo an yi akan lokaci ba, sai a ce sai a tara sai wata shekarar, amma idan akwai jajircewar al’umma suna bibiya yau da gobe in Allah ya yarda  zata taimakawa sanarwa shugabanni abinda al’umma ke buƙata.

Cikin mutanen da aka karrama sun haɗa da Alhaji A A Rano da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya. Hon. Alhasan Rurum da sauran mutane da suka haɗa da jami’an tsaro da ‘yan kasuwa da sauran masu muƙamai a ɓangarori da dama ‘yan yankin.

By ukarofi