Abuja: A wani karon, hatsari ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a gadar Karu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mutane da dama ne suka rasu a gadar Karu da ta haɗa Jihar Nasarawa da Birnin Tarayya Abuja a yayin aukuwar hatsarin tirela.

Wani shaida ya ce, hatsarin ya faru ne tsakanin tirelar da wata mota da ke ɗauke da ruwan leda, wato pure water.

Hatsarin ya auku ne kwana ɗaya da yin makamancinsa da ya yi sanadin rasa rayukan mutane da dama a wajen, wanda ya haddasa damuwa game da zirga-zirgar al’umma cikin lumana a yankin.

Wannan shi ne karo na uku da ake samun hatsari mai muni a hanyar, wadda ta haɗa Nyanya zuwa Keffi a Nasarawa da kuma kai wa zuwa Jihohin Benue da Filato.

By Babaji