Gwamnatin Kano ta dakatar fina-finan Hausa masu dogon zango

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A ƙoƙarin ta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sau da ƙafa tare da ƙara ɗora masana’antar kannywood a kan saiti, Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alh. Abba El-mustapha ta ɗauki wani gagarun mataki domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai ba tare da cika ƙa’idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowanne fim gabanta a tantance shi kafin ya isa ga idanun al’umma, inda ta dakatar da wasu manyan fina-finai har guda 22 daga sakasu a kafafen intanet ko gidajen talabijin.

Shugaban hukumar Abba El-mustapha ne ya bayyana wannan mataki biyo bayan tattaunawa da manyan jami’an hukumar tare da dogon nazari domin kawo ƙarshen ƙorafe ƙorafen da hukumar take yawan karɓa dan ƙara inganta ayyukan hukumar tare da masana’antar kannywood.

Abdullahi Sani Sulaiman jami’in yaɗa labaran hukumar ya bayyana fina-finai da aka dakatar kamar haka:

  1. Ɗakin Amarya
  2. Mashahuri
  3. Gidan Sarauta
  4. Wasiyya
  5. Tawakkaltu
  6. Mijina
  7. Wani Zamani
  8. Labarina
  9. Mallaka
  10. Kuɗin Ruwa
  11. Boka Ko Malam
  12. Wa ya san Gobe
  13. Rana Dubu
  14. Manyan Mata
  15. Fatake
  16. Gwarwashi
  17. Jamilun Jiddan
  18. Shahadar Nabila
  19. Daɗin Kowa
  20. Tabarma
  21. Kishiyata
  22. Rigar Aro

Ya ƙara da cewa doka ce ta bawa hukumar damar tace duk wani fim tare da lura da ayyukan ƴan masana’antar kannywood matsawar suna da rajista da hukumar a ko ina suke. A saboda haka ana shawartar masu ɗaukar nauyin wannan fina-finai da su tabbatar da sunbi wannan doka ta dakatarwa tare da tsayar da saka wannan fina-finai a gidajen talabijin ko kafar intanet.

Kazalika, ana sanar dasu cewa su miƙa fina-finansu ga hukumar domin tantance su tare da basu shaidar inganci ta tacewa nan da sati ɗaya mai zuwa wato daga LITININ, 18 ga watan Mayu, 2025 zuwa 25 ga Mayu, 2025 domin gujewa fushin doka.

A ƙarshe hukumar ta nemi haɗin kan dukkannin gidajen talabijin da hukumar dake lura da kafafen yaɗa labarai ta Nijeriya wato NBC kan su cigaba da taimakawa hukumarsa domin samun nasarar abinda ta saka a gaba da cigaban Jihar Kano da masana’antar kannywood.

By ukarofi