
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba shi da burin tsayawa takara a matsayin abokin karawar Shugaba Bola Tinubu ba a zaɓen 2027.
A wata hira da BBC Pidgin kamar yadda NigerianKicker ta ruwaito, Wike ya yi watsi da batun zama abokin hamayyar Shugaban Ƙasar, yana mai jaddada goyon bayansa ga gwmanatin na yanzu.
Hakan ya biyo bayan kiran da jam’iyyar PDP ta yi masa na zaɓo ɗan takara daga yankin Kudu, lamarin da ya haifar da cece-kuce acikin al’umma.
Saidai, a lokacin da ya ke magana kan batun, Wike ya ce ba zai yiwu ya fito takara a kujera ɗaya da wanda ya ke yi wa aiki ba, inda ya yi furuci kamarhaka; “ban zan tsaya ba a 2027”, inji shi.
Tsohon gwamnan na Jihar Ribas, wanda ɗaya ne daga cikin jiga-jigan gwamnatin Shugaba Tinubu, ya bayyana cewa ba ya adawa da mai gidan nasa don haka babu hikima wajen zama abokin gwabzawarsa.
Kalaman Ministan sun nuna cewa babu wani rikicin siyasa da ke tsakanin sa da Tinubu a yayin da ake cigaba da sauye-sauyen jam’iyyu a ƙasar.
