Tinubu ya amince da bada lasisin ayyukan haƙar mai na Kolmani

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya amince da bada lasisin gudanarwa na aikin haƙo mai a yankin Kolmani dake tsakanin Jihohin Bauchi da Gombe.

Ƙaramin Ministan Albarkatun mai, Sanata Heineken Lokpobiri ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sansani na dindindin na aikin mai da gas a Ƙaramar Hukumar Alƙaleri dake Bauchi.

A sanarwar da mai bai wa Ministan shawara kan harkar yaɗa labarai, Nneamaka Okafor ta fitar, ya ce hakan ya samu ne a ƙoƙarin gwamnati na haɓaka harkar samar da mai a dukkan wurare masu albarkatun mai a sassan Nijeriya.

Ministan ya ce, Gwamnatin Tarayya ta duƙufa wajen tabbatar da amfani da dukkan ɓangarorin albarkatun makamashi, wanda hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da faɗaɗa damanmakin samun kuɗaɗen shiga ga gwamnati.

Ya kuma yaba wa gwmanatin jihar Bauchi bisa haɗa hannu da manufofin makamashi na Gwmanatin Tarayya wajen samar da tashar man, lamarin da ke nuna jajircewarta wajen gina ɓangaren.

A watan Nuwamban 2022 ne aka fara ƙaddamar da aikin haƙo man na Kolmani, wanda ya zama na farko a Arewacin Nijeriya a wani yanki dake tsakanin Jihohin Bauchi da Gombe.

A makon da ya gabata ne ɗaya daga cikin jagororin Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Bayo Ojulari ya bayyana cewa, tashar haƙo man za ta koma aiki nan ba da jimawa ba, lamarin da ya ce zai sa kamfanonin da ke rufe a sake buɗe su domin cigaba da ayyukansu.

By Babaji