Abuja, Kano, Kaduna da Filato na fuskantar mummunan hatsarin Korona

Daga BASHIR ISAH

Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Yaƙi da Annobar Korona (PSC) ya ayyana wasu jihohi guda shida, ciki har da Birnin Tarayya, Abuja, da ke fuskantar mummunan hatsarin korona tare da cewa akwai buƙatar jihohin su matse ƙaimi dangane da sha’anin yaƙi da cutar korona yayin bikin Babbar Sallah.

Kwamiti ya bayyana haka ne biyo bayan wani nau’in koronar da aka gano a jihar Delta da kuma yadda ake samu ƙaruwar masu harbuwa da annobar a faɗin ƙasa.

Shugaban kwamitin  kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai Asabara da ta gabata a Abuja.

Mustapha ya lissafo jihohin da lamarin ya shafa da suka haɗa da Lagos, Oyo, Rivers, Kaduna, Kano Filato da kuma Birnin Tarayya, Abuja.

Ya ƙara da cewa, jan hankalin da aka yi wa jihohin da lamarin ya shafa wani mataki ne na hana yaɗuwar annobar korona karo na uku.

Haka nan, ya gargaɗi sauran jihohin ƙasar nan da su zauna cikin shirinsu sannan su ci gaba da kiyaye duka dokokin da aka shimfiɗa don yaƙi da annobar.

A ƙarshe, kwamitin ya ba da shawarwarin da ya kamata al’umma su kiyaye a lokacin bikin sallah da suka haɗa da; yin amfani da masallatan Juma’a wajen sallar Idi domin rage cunkoso a manyan masallatan idi, dakatar da hawan sallah da kuma taƙaita yawan jama’a wajen sauran tarurruka.