Shugabannin jam’iyar babbar adawa na ADC a Katsina sun tsayar da Ahmad Babba Kaita a matsayin ɗan takarar gwamna a zaɓen 2027.
Matsayar ta fito ne bayan wani muhimmin taro da shugabannin jam’iyyar na jihar suka gudanar tare da manyan jagororin ADC na ƙasa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da shugaban jam’iyar na ƙasa David Mark.
Haka kuma, taron ya amince da Ahmed Aminu Yar’adua a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna, lamarin da ya nuna cewa jam’iyyar ta fara shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da wuri.
Sai dai wannan ci gaba ya haifar da tambaya mai ɗaukar hankali a fagen siyasar Katsina:
Shin Ahmad Babba Kaita zai iya ƙalubalantar tare da kayar da Dikko Raɗɗa na jam’iyar APC kuma gwamnan jihar mai ci yanzu a zaɓen gwamnan Katsina na 2027?
Ko ADC za ta iya karya ƙarfin APC a jihar Katsina? Ko kuma nasarorin da gwamnatin Dikko Raɗɗa ke ikirarin samu za su ci gaba da ba shi goyon bayan jama’a?
Haka kuma jam’iyar ADC ta tsaida tsohon darakta janaral na hukumar DSS Lawal Musa Daura a matsayin ɗan takarar kujerar sanata na shiyar Daura a zaɓe mai zuwa.
Haka kuma sanata Abubakar Sadiq Yar’adua shima ɗan takarar sanata shiyar Katsina da kuma Birgediya Maharazu Tsiga mai ritaya ɗan takarar kujerar sanata a shiyar Funtua.
Haka na zuwa a yayin da tsagin jam’iyar a ƙarƙashin shugabancin Musa Usaman Wamba ta fitar da Salisu Lawal Uli a matsayin ɗan takarar jam’iyar na ADC a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Katsina.
