ADC na cigaba da samun karɓuwa a ƙaramar hukumar Karu – Hon. Teghtegh

Spread the love

DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya

Shugaban sabuwar jam’iyyar ADC na ƙaramar hukumar Karu jihar Nasarawa Hon. John T. Teghtegh yace a halin yanzu jam’iyyar ta samu sama da magoya baya 70,000 waɗanda aka yi musu rajista a ƙaramar hukumar ta Karu kaɗai.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a gidan sa da ke Uke a Karu.

Yace bayan wannan ɗimbin magoya baya da jam’iyyar ke cigaba da samu a ƙaramar hukumar a yanzu, har ila yau jam’iyyar kawo yanzu ta kuma samu sama da ‘yan takara 20 wadanda suka fito neman kujeru daban daban a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC ɗin a matakin ƙasa da jihar. Hakan a cewar sa wani manuni ne ƙarara cewa sabuwar jam’iyyar ta samu karɓuwa matuƙa a yankin dama jihar ta Nasarawa baki ɗaya.

Hon. John ya kuma ƙara da cewa duka waɗannan yan takaran da ke fitowa ƙarƙashin ADC ɗin a duka matakai da suka hada da kujerar gwamnan jihar da na sanata da na majalisar wakilai ta tarayya da na jihar da ƙananan hukumomin jihar da sauran su duk mutane ne masu daraja da mutunci cikin al’umma waɗanda ke da kyawawan niyar samar da shugabanci nagari ga al’ummar su. Ya buƙaci waɗanda ba su shiga jam’iyyar ba da su shigo ayi tafiyar da su, domin jam’iyyar a yanzu ta zamo jirgin annabi Nuhu da zai tsirar da kowa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Hon. John T. Teghtegh ya kuma bayyana cewa a yanzu duka mazaɓu 11 da ke ƙaramar hukumar Karu ɗin suna da shugabanni na jam’iyyar waɗanda a yanzu suna cigaba da karɓar sabbin mambobi da suke canja sheka zuwa ADC ɗin daga wasu jam’iyyun adawa.

Dangane da ƙalubalai da jam’iyyar ke fuskanta a yanzu a ƙaramar hukumar ta Karu sai shugaban ya bayyana cewa ƙalubalan bai wuce na kasancewar sabuwar jam’iyyar ta ƙunshi ɗimbin magoya bayan wasu jam’iyyun adawa da ke cigaba da kwararowa jam’iyyar da hakan yasa suna ɗan samun ƙalubalai amma a yanzu hakan suna fahimtar junansu kuma sun zama ɗaya duk da banbancin siyasa da ada ke tsakanin su.

By ukarofi