DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya
An buƙaci ‘yan siyasa da shugabanni a duka matakai da masu hannu da shuni a jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya su riƙa tallafa wa ayyuka na musamman da ke ɗaukaka harkokin addini a duk inda suka tsinci kansu.
Ɗan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a mazaɓar Akwanga da Wamba da kuma Nasarawa-Eggon a jihar Nasarawa Hon. Tony Bala Shama wanda aka fi sani da TBS ne yayi wannan kira a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin mu a wajen wani taron ƙaddamar da babban masallacin Andaha da ke ƙaramar hukumar Akwanga.
Yace kira ya zama wajibi idan aka yi la’akari da ɗinbin albarkun Ubangiji da rahamar sa tun a nan duniya da kuma gobe ƙiyama da duk wanda ya aiwatar da aikin zai samu.
Hon. Tony Bala Shama ya kuma yaba wa wanda ya gina masallacin wato wani mai aikin taimako da aka fi sani da Adamu Custom inda yace tabbas hakan wani abun gwaninta ne da yakamata kowa ya yi koyi da shi.
Hon. Tony Bala Shama ya kuma yi amfani da damar inda yayi kira na musamman ga al’ummar jihar baki ɗaya musamman Kirstoci da Musulmai su cigaba da haɗa kai suna zaman lafiya da son juna kasancewar duk da banbance-banbancen siyasa da addini da sauran su da ke tsakanin su kada su manta su yan uwan juna ne.
Har ila yau da yake amsa tambayar wakilin mu dangane da ire-iren salon wakilcin sa idan ya samu damar wakiltar shiyar a shekarar 2027 dake tafe, Hon. Tony ya bayyana cewa daga cikin ɗimbin ayyukan cigaba da zai tabbatar ya kawo wa al’ummarsa akwai wannan batun ba da fifiko ga duk wani aikin ɗaukaka tare da bunƙasa harkokin manyan addinan nan biyu tare da tabbatar da haɗin kan su da kuma uwa uba zaman lafiya .
A ƙarshe sai ɗan takarar ya kuma yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da kafa tubalin zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin duka addinai a jihar da hakan ne yasa a cewarsa kowanne shugaba ke yin koyi da shi a yanzu.
