Kotu ta bada izinin binciken takardun karatun Ministan Cikin Gida, Tunji-Ojo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja, ta amince da buƙatar ƙorafin da aka shigar mata da ke neman ta bayar da izinin yin bincike akan sahihancin takardun karatun Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

Mai Shari’a Binta Nyako a ranar Juma’a ta amince da hakan a takardar da ɗan gwagwarmaya Emorioloye Owolemi ya gabatar domin neman gano sahihancin takardar kammala sakandarensa ta WAEC.

Lauyan ɗan gwagwarmayar, Philemon Yakubi (SAN) ya miƙa takardar bisa hukuncin dokar ‘yan samun bayanai sashe na 1, 20 da na 21 a kundin 2011.

A yayin hukuncin, Alƙalin ta ba lauyan izinin cigaba da gudanar da binciken gano ainihin sahihancin shaidar WAEC ɗin ministan..

Daga nan ne mai shari’ar ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga watan Maris.

A wani labarin kuma, wata Babbar Kotu a birnin tarayyar ta hannun Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta ƙi amince wa buƙatar Owolemi ta duba sahihancin takardar kammala hidimarsa ta NYSC.

Buƙatar, wadda aka ƙi karɓar, ta nemi a ba ta damar tantance takardar NYSCn ministan, wanda ya yi karɓar ta a shekarar 2006.

By Babaji