ADC: Peter Obi ya yi ganawar sirri da Gwamna Bala a Bauchi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fitaccen ɗan siyasa a jam’iyyar ADC kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya kai ziyara Jihar Bauchi inda ya gana da Gwamnan jihar, Bala Mohammed, a wani taro na sirri da aka gudanar a ranar Alhamis.

Ganawar ta gudana ne a ɗakin taro na musamman da ke Gidan Gwamnati, ba tare da bayyana cikakken dalilin haɗuwar ba, lamarin da ya ƙara janyo hankalin masu bibiyar harkokin siyasa a ƙasar.

Rahotanni na nuni da cewa wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin yiwuwar sauyin sheƙa na Gwamna Bala Mohammed gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Ana sa ran shugabannin biyu za su yi wa manema labarai bayani bayan kammala ganawar, duk da cewa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani cikakken bayani da aka fitar.

Gwamna Bala Mohammed, wanda kuma shi ne Shugaban ƙungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP, ya taɓa nuna yiwuwar sauyin tafiyar siyasa a wata ganawa da ya yi da wakilan ADC ƙarƙashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, a ranar 31 ga Maris.

Sai dai kuma, al’amuransa na siyasa sun ci gaba da janyo muhawara, musamman bayan wasu ganawa da ya yi da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da kuma Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.

Masu sharhi kan harkokin siyasa na kallon wannan ganawa a matsayin wata muhimmiyar alama da za ta iya sauya yanayin siyasar ƙasar, musamman idan aka yi la’akari da tasirin Gwamna Bala Mohammed a cikin PDP da kuma yiwuwar sauya akalar haɗin gwiwar jam’iyyu kafin zaɓen 2027.

By ukarofi