Afam Osigwe wanda shine tsohon sakataren ƙungiyar lauyoyin Nijeriya ya zama sabon shugaban ƙungiyar a zaɓen da aka gudanar.
Zaɓen an yi shi ne ta hanyar yanar gizo. Zaɓen ya fara ne tun 12 na safiyar Asabar zuwa 11:59 na ranar Lahadi.
Osigwe yayi nasara samun ƙuri’u 20,435, yayin da wanda yayi na biyu ya samu ƙuri’u 10,998.
Osigwe zai amshi shugabancin ne daga hannun Yakubu Maikyau(SAN) wanda wa’adin mulkin shi ya zo ƙarshe.
Sebatian Anyia shine ya zamo mataimaki na farko na ƙuri’u 12,114. Sai kuma Bolatumi Animashaun ya zama mataimaki na biyu da ƙuri’u 26,534. Yayin da Zainab Garba ta yi nasarar zama mataimakiya ta uku.
Dr Mobolaji Ojibara ya zama sabon sakatare,Mrs Blessing Udofa ita ta zamo ma’aji na ƙungiyar.
