Lafiya Jari: Yaro sabon mutum

Spread the love

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

Jarirai kyauta ce daga Allah. Abin sha’awa da birgewa na tattare da su.

Matso in fada maka wasu abubuwa game da jinjiri sabuwar haihuwa. Zan faɗa maka wasu keɓance keɓance na jarirai wanda babban mutum bashi da su.

1. Kamar yadda za aka iya gani da idanunka, jariri na da katon kai, wanda ya lashe kaso ashirin da biyar na girman jikinsa. Wato idan za a raba jikin jariri kaso ɗari, to kaso ashirin da biyar girman kansa ne

2. Sauran sassan jikin jariri na da kaso 75 amma duk da haka yafi fitar da hucin zafi ta kansa. Wato kaso talatin da shida na hucin zafin da ke fita daga jikin jariri da kansa ya ke fitowa.

3. Jariri idan yana jin sanyi baya rawar ɗari. Kai babba kaine ka santa, shi bai san wannan ba. Akwai wani tsari da Allah ya yi wa jarirai ta yadda za s uke ƙone wani kitse na musamman da zai dinga ɗumama musu jikinsu daga ciki.

4. Jariri na iya numfashi a lokacin da yake shan nono. Tirƙashi! Shi ko babban mutum ko ruwa zai sha, ko kuma zai haɗiyi wani abu, sai numfashinsa ya ɗan katse kafin ya sha/.

5. Jariri baya san damuwa ko kaɗan. Irin yadda babba ya ke haƙilo wajen ganin cewa ya yaƙi duk wani abu ƙarami ko babba da zai iya kawo masa cikas wajen kasancewa a raye, jariri ko a jikinsa! Misali, idan mura ta kama shi, musamman irin mai toshe hancin nan,bai zai damu da ya buɗe bakinsa domin yayi numfashi ba.

Waɗannan bayanai na da amfani domin za a iya amfani da su wajen ceto rayuwar jariri musamman idan bashi da lafiya.

Ku tara a rubutu nagaba.

Naku,

Mustapha Ibrahim Abdullahi

(c) MIAbdullahi

By ukarofi