Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Mutumin da ya fi kowa kuɗi a nahiayr Afirka, Aliko Ɗangote ya bai wa jama’a da dama mamaki tun bayan da ya sanar da cewa ba shi da gida a ƙasashen waje.
Ɗangoto ya kuma sanar da cewa gidajensa biyu ne rak sannan kuma gidan haya yake sauka a duk lokacin da ya je Abuja, babban birnin Nijeriya.
Ta ƙara da cewa, “Ban taɓa ganin wanda ya kai mahaifina aiki tuƙuru ba, wani lokacin ina mamakin yadda ba ya kasala.
“Ina fata muna da wasu maza kamar mahaifina a Nijeriya, ƙasar za ta yi kyau,” inji ta.
Shi masanin masana’antu ne wanda ya kafa kuma ya jagoranci Ɗangote Cement, babban mai samar da siminti a nahiyar. Ya mallaki kashi 85 cikin 100 na simintin Dangote da ake sayar da shi a bainar jama’a ta hannun wani kamfani.
Aliko Ɗangote ne dai attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka kamar yadda mujallar Forbes ta fitar a karo na 13 a jere duk da irin aalubalen tattalin arziƙin da Nijeriya ke fuskanta.
Dukiyar Ɗangote ta ƙaru da dala miliyan 400 a shekarar da ta gabata, inda yawan arzikinsa ya kai dala biliyan 13.9 kamar yadda mujallar Forbes a lokacin.
