Afirka ta farka kuma ta cancanci a zuba jari cikinta – Shettima

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan, a yayin da yake gabatar da jawabi wajen taron tattalin arzikin duniya na shekarar 2025 da ke gudana a birnin Davos na ƙasar Switzerland.

Kashim Shettima ya jaddada cewa Najeriya a shirye take da karɓan kasuwanci da ‘yan kasuwa ƙarkashin sabbin dabarun da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samar a ƙokarinsa na ganin ƙasar ta zama cibiyar zuba jari a Afirka

Shettima ya bayyana yadda ake samun bunƙasar saka hannun jari a ƙasar inda ya roƙi masu zuba jarin da su yi watsi da labaran ƙanzon-kurege da ake yaɗawa kan rashin tsaron dukiyoyin masu zuba Jari a Najeriya

Mataimakin ya ce a yanzu Najeriya na hannun ƙwararru duba da matsayin shugaban ƙasar na gogaggen masani a kan kasuwanci da Mataimakinsa wanda ya share shekaru 20 yana aikin banki,

Mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada irin ƙarfin da nahiyar Afirka ke da shi, inda ya bayyana cewa nahiyar ta farka kuma a shirye ta ke ta
ɗauki matsayinta a duniya, yana mai ambato kalaman marigayi shugaban Najeriya, Janar Murtala Mohammed, inda yake cewa Afirka dattijiyar nahiya ce da ba ta cancanci a sanya ta a sahun matasan Nahiyoyi ba.

Jim ƙaɗan bayan kammala tallata Najeriya da Afirka a matsayin wuraren zuba jari, Kashim Shettima ya halarci wani zaman da wasu shuwagabannin ƙasashen Afirka da suka haɗa da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da shugaban Botswana Duma Boko, zaman na su ya biyo bayan buƙatar ƙarfafa dangantakar dake tsakanin ƙasashen Afirka da haɗin gwiwar tattalin arziki.