NSCDC ta kama ma’aikacin KEDCO bisa satar kayan wutar lantarki a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Jami’an tsaron NSCDC sun kama wani ma’aikacin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta (KEDCO), Aliyu Muhammed, bisa zarginsa da ɓarnatawa da kuma satar mitocin wutar lantarki a gidajen jama’a.

Jami’an tsaro na musamman na hukumar ta NSCDC sun kama Mohammed mai shekaru 38 a Tudun Wada Quarters dake ƙaramar hukumar Daura bayan samun bayanan sirri kan ayyukan sa.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar NSCDC a jihar Katsina, SC Buhari Hamisu ne ya sanar da haka yayin da yake gabatar da wanda ake zargin da yammacin ranar Talata, hukumar ta bayyana cewa asirin ma’aikacin KEDCO ya tonu bayan da ya saci mitar wutar lantarki a gidan wani Alhaji Lawal Gadi a ranar 16 ga Janairu, 2025.

Kakakin hukumar ya ce: “Aliyu Muhammad ma’aikaci ne da ke aiki da sashin kula da mitoci na ofishin KEDCO da ke Daura. Yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa aikata laifin kuma ya bayyana cewa a ranar Laraba 15 ga watan Janairu, 2025, da farko ya je gidan Alhaji Lawal Gadi da ke Tudun Wada don raɗin Kansa.

“Ya kuma sake komawa washe gari da yamma, don ya ga yanayin yadda unguwar take sannan bayan ƙarfe 7:00 na yamma ya shiga gidan ya cire mita. An samu mitar tare da shi a matsayin shaida. A halin yanzu dai ana kan binciken wanda ake zargin, kuma za a ci gaba da bin diddiginsa a yayin da ake tuhumar sa.” In ji kakakin hukumar.

Kakakin hukumar ya bayyana cewa hukumar NSCDC a jihar ƙarƙashin jagorancin kwamandan rundunar, Aminu Datti Ahmad, ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen magance ayyukan ɓarayi da masu yin zagon ƙasa ga tattalin arziki da dai sauran masu aikata laifuka a jihar.