Afirka ta nuna damuwa ko Turai za ta iya cika alƙawurran da ta ɗauka a wajen taron ƙolin Turai da Afirka

Daga CRI HAUSA

A ranar 18 ga wata, aka kammala taron ƙoli tsakanin ƙungiyar tarayyar Turai EU da ƙungiyar tarayyar Afirka wato AU a birnin Brussels na ƙasar Belgium, inda aka cimma wasu nasarori a ɓangarorin da suka shafi sake tsugunar da al’umma, da kiwon lafiya, ciki har da wani shirin zuba jari ga ƙasashen Afirka da EU ta sanar, wanda ke ƙunshe da kuɗin EURO biliyan 150.

Masanin dangantakar ƙasa da ƙasa daga ƙasar Kenya, Cavins Adhill ya yi tsokaci kan nasarorin taron ƙolin, inda a cewarsa, duba da yadda nahiyar Afirka ke matuƙar buƙatar zuba jari a fannin kiwon lafiya, shirin na EU yana da babbar ma’ana. Amma kamar yadda malam Bahaushe kan ce, kyan alƙawari cikawa. Har yanzu, ba a tabbatar waɗanne fannoni wannan shirin zai goya musu baya, kuma waɗanne ƙasashe ne za su ci gajiyar shirin ba, da lokacin kammala shi, dukka ba a sani ba.

Mista Adhill ya ƙara da cewa, al’ummar Afirka na son samun ci gaba, amma ba su buƙatar zance fatar baki kawai wanda ke haɗe da barazana ko wasu sharuɗɗa. Idan mun dubi yadda aka cika alƙawurran da EU ta dauka a wajen tarukkan kolin na baya, muna iya ganin cewa, babu wani abun da zai sa ƙasashen Afirka su sake amincewa, EU ta riga ta kafa wani sabon tsarin raya dangantaka tare da Afirka, wanda ke da adalci da samun moriyar juna da samar da ci gaba mai ɗorewa.

Fassarawa: Murtala Zhang