Akwai buƙatar ɗaukar matakai kan durƙushewar lantarki daga shugabannin Arewa – Shugabar NFHA

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

An bayyana cewa bala’o’i uku da suka afkawa Arewa wanda idan wasu ƙasashen ne masu kishin al’ummar su za a iya daƙile su, domin ilimi abu ne mai yawa kuma tun a da ana amfani da shi don taƙaita wani bala’i wanda ka iya faɗawa al’umma kuma duk mai ilimi da son gaskiya yasan wannan gaskiya ne, “don haka akwai tsananin buƙatar shugabannin mu na Arewa daga kan gwamnoni, sanatoci, ‘yan majalisar wakilai, ‘yan majalissar jihohi, sarakuna, ‘yan kasuwa, masana a kowane fanni na rayuwa, malaman addini da sauran shugabanni na Arewa akwai buƙatar ɗaukar matakin daƙile bala’o’in da ke afkawa, musamman a wannan lokaci da mummunar ambaliyar ruwa ta afkawa Maiduguri da kuma mummunar gobara da ta afkawa Majiya Jihar Jigawa sai kuma durƙushewar wutar lantarki da ta afku tun wajen 20 ga watan Oktoba 2024.

“Akwai maƙarƙashiya a wannan durƙushewar wutar lantarki domin kuwa ya kassara Arewa da al’ummar ta musamman ta fannin tattalin arziƙi, wanda ke buƙatar ɗaukar matakan duk irin waɗannan bala’o’i na ambaliyar ruwa, gobarar da ta ci ɗimbin rayuka a Jigawa, Nijeriya da sauransu.”

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Hajiya Aisha Abdussamad, Shugaban ƙungiyar masu sufuri ta NFHA National Freight Haulies Association ta ƙasa reshen Jihar Kano a lokacin da ta ke ganawa da Jaridar Blueprint Manhaja a Kano.

Haka kuma ta ce daga waɗannan abubuwa kamar na gobara za ka ga ana ta kai gudummawa abinci da kuɗaɗe da sauran gudummawa, abu ne mai kyau a rayuwa amma ɗaukar matakai ka da bala’i ya faru ya fi akai gudummawar abinci amma fa idan ka tashi daga wata jihar kaje wata jihar ka ba da gudummawa su ma al’ummarka na buƙatar gudummawa, domin suna cikin yinwa, fatara, talauci da mutane ke rasa rayukansu saboda yunwa, don haka su na buƙatar kuɗi da sauransu, domin rayuwa kan da aka rasa a ambaliyyar ruwa da gobara da aka rasa za su dawo ne, sai dai a ce Allah ya jiƙan su da rahama, haka dukiya ba za ta dawo ba, sai dai wata don haka muna roƙon shugabanninmu na Arewa su tashi tsaye wajen kawo ɗauki musamman da abubuwa da ke faruwa da a arewa akai akai, tun daga kan rashin tsaro talauci, fatara, rashin aikin yi, wanda ko abun da ya faru na rasuwar ɗin bun mutane a jigawa, tushansa talauci ne, wanda kuma za’a iya kawar da shi a wannan ƙasa da Allah ya albarkanci wannan ƙasa da arziƙi.

Har ila yau ta ja hankalin iyaye maza da mata, shugabanni da malaman addini kan su tashi tsaye wajen daƙile abubuwan ɓarna da ‘yan mata da samari suke yi babu kunya babu tsoron Allah na aikata fasiƙanci,  harkar daudu, ga na mace da mace a wannan zamani.

Ta ce wajibi ne a tashi tsaye wajen kawar da ɓarna da bayyana ta duk da a nan Kano hukumar Hisbah na ƙoƙari amma ta ƙara ruɓanyawa kuma a samar da doka ta hana bayyana duk wani abu mai kama da fasiƙanci, kamar yadda yake a ƙasar Ghana akwai abinda idan aka gayi a bainar jama’a za a kamata a hukuntaka, wanda ana ganin ma cewa a gana idan aka samu tuzuru, ko gwarangwami da makamanta su, za a iya kamata a hukunta ka domin dai daƙile ɓarna a bayan ƙasa wanda duk al’ummar da ta ɗaurewa fasiƙanci ko mu’amala namiji da mace ba tare da aure ba wannan al’umma ko ƙasa na iya durƙushewa.

Don haka ta ce akwai buƙatar a yi kishin al’umma, a yi kishin ƙasa, domin ci gaban ƙasar mu Nijeriya ta kowacce fuska a wannan lokaci da ƙasar ke tsananin buƙatar zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun tattalin arziƙi.

By ukarofi