Akwai buƙatar mutane su iya bambance matsalar nakasa da ta aljannu – Fatima Bello

“Iyaye su rage amfani da magungunan gargajiya ga yara masu matsalar nakasa”

Daga ABUBAKAR M. TAHEER

Fatima Bello matashiya ce da ta ke taimakon yara masu buƙatar ta musamman, inda ta buɗe gidauniyar tallafa musu mai suna Haske Children Foundation. A cikin wannan tattaunawa da wakilin Manhaja, Abubakar M Taheer ya yi da ita, ta nuna takaicin ta kan yadda al’umma suka ɗauki masu bukata ta musamman a matsayin wani abu da ya shafi aljannu, dama wasu batutuwa da ya shafi taimakon masu buƙata ta musamman. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: DA farko za mu so ki gabatar mana da kanki ga masu karatunmu.

HAJIYA FATIMA: Assalamu alaikum warahamullah. Sunana Fatima Bello, kuma ni an haifeni a Jihar Katsina. Na yi karatun digiri ɗina na farko a kan ilimin ‘Sociology’, haka kuma na sake samun wata shedar digiri akan ‘Communication Studies’. Daga nan na ci gaba da karatu inda na karanci ‘International Relationship’ da Disability Studies’ a matsayin digiri na biyu.

Yaushe ne ki ka buɗe Haske Children Foundation?

To Alhamdulillah, kusan zan ce na fara gudanar da ita gidauniyar Haske Children Foundation ne kusan shekaru 15 da suka gabata, amma a lokacin na rinqa tunanin cewa, bari in bari idan na fara aiki na tara kuɗi bayan na yi ritaya sai na buɗe, amma a sai na sake wani tunanin inda ya zama na ci gaba da gudanar da shi gadan-gadan a a shekarar 2020. Kuma dai zuwa yanzu muna samun nasarori ba ƴar kaɗan ba.

Yawancin yaran da ke fama da buƙata ta musamman ana kallo kamar ko aljani ya shafe su ko wani abu daban wanda hakan kan jawo tsangwama gare su. A matsayinki ta mai sani irin wannan, ya ki ke kallon wannan lamarin?

To a gaskiya wannan babbar matsala ce da ta ke damun al’ummarmu, musamman ma a Ƙasar Hausa, za ka ga ana yi wa masu buqata ta musamman wani kallo na daban, kamar su ne suka jama kansu, wasu kuma ana kallon sun haɗu da ciwon aljannu ne, wani lokacin a rinqa kashe kuɗi wajen neman maganin gargajiya.

Wanda kuma kaga hakan ba ƙaramar matsala ba ce, abinda kullum muke fata ko muke ƙoƙarin wayar da kan mutane shi ne, su gane rashin iya maganar yaro, ko rashin gani, ko matsalar ƙwaƙwalwa dukkan su suna da buƙatar magani ne na musamman ba kuma lallai sai aljannu ne suke shiga jikin mutum ba. Wani lokaci jinya ce Allah Yake ɗora wa yaro tun yana cikin mahaifiyarsa.

A haka kuma wani lokacin ko a makarantar za ka ga ana yima yara masu buƙata ta musamman kallon wasu na daban saboda nakasar su.

Wannan tasa a kullum muke kira ga iyaye da su rinƙa jan yaransu masu fama da wannan matsala jiki suna kwantar musu da hankali, wani lokaci idan aka yi dace da shan magungunan sai kaga yaro ya samu lafiya.

Kasancewar gidauniya irin wannan ta masu buƙata ta musamman na buƙatar kuɗi wajen wayar da kai dama bada magani. Ya ki ke samar da kuɗaɗen da ki ke wannan aikin?

To Alhamdulillah, maganar gaskiya za ka tarar cewa, irin wannan matsalar masu buƙata ta musamman tana buƙatar kuɗi ne sosai wajen wayar da kai da ma magungunansu, yawanci yaran sun fito ne daga gidan masara ƙarfi, wani gidan ba ma su da abincin da suke ci.

Kaga mutumin da yake nema abinda zai ci ina zai iya biyan maƙudan kuɗaɗe na magani. Wannan tasa mukan buɗe ƙofofin mu wajen ‘yan’uwa da abokan arziki domin samun kuɗin taimaka musu.

A haka mai taro da sisi mukan haɗa mu tasar da wani abu sai mu shiga aikin bada agaji. Kuma Alhamdulillah gaskiya ƴan’uwa da abokan arziki kusan su ne suke gudanar da wannan babban aiki na bada kuɗinsu wajen taimaka wa masu buƙata ta musamman. Amma a yanzu muna ƙoƙarin faɗaɗa abin namu ya zama muna samun kuɗin shiga daga kamfanoni da ɓangarorin gwamnati.

Waɗanne nasarori ne za a ce kun samu a wannan tafiya?

To Alhamdulillah, nasara kusan kullum lissafata muke yi, don mun fara shirin faɗaɗa ayyukanmu ya zama ko’ina a faɗin ƙasar nan. Ya zuwa yanzu muna bada taimako ne a jihohin Arewacin ƙasar nan. Amma mun fara tunanin faɗaɗa aikin da yardan Allah.

Haka kuma a wannan shekarar ta 2023 muna burin ko ince tsarin bada magani kyauta ga masu buƙatar ta musamman dama bada ɗan kuɗin kashewa ga iyaye matan domin ci gaba da riƙe kansu.

Haka kuma Alhamdulillah, ina jin daɗin yadda ‘yan’uwana da abokan arziki suke bada nasu gudunmawa, wasu dasu akan yi aikin bada agaji ina nufin su kan bada lokacinsu da ilimi da Allah ya hore musu domin tallafa wa masu buƙata ta musamman.

Wane irin ƙalubalai ne ku ke fuskanta zuwa yanzu?

To gaskiya kamar yadda ba faɗa maka a baya, babban ƙalubalan mu shi ne ƙarancin kuɗin gudanarwa wanda shi ne yakan tsaida mana aikin namu. Amma muna ƙoƙarin lalubo hanyoyin rage rashin kuɗin da muke fama da shi.

Daga ƙarshe wane kira ki ke da shi?

To a ƙarshe ina kira ga iyayen da su rinƙa kai yaransu masu fama da buƙata ta musamman zuwa asibiti domin lalubo jinyar da ke damunsu. A dena ɗora wa aljannu komai.

Haka kuma iyaye su rage amfani da magungunan gargajiya musamman ga masu buƙata ta musamman domin kada a sake jefa yaro cikin matsalar da ta fi ta da. Yawanci kusan shi ne abinda yake bamu wahala. Za ka ga iyayen sukan kafe cewa, su shi ne abinda suka saba da shi, to a rinƙa ragewa, ana neman masana lafiya.

Haka kuma ina kira ga kamfanonin da masu hannu da shuni da ma uwa uba gwamnati, da su shigo cikin irin wannan ayyukan cigaban al’ummar domin samar da cigaba mai ɗorewa.

Mun gode.

Ni ma na gode ƙwarai.