Hausawa mazauna jihohin kudu: Gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah

Manhaja logo

Daga RAHMA ABDULMAJID

Abubuwa uku ne ɗauke a cikin wannan gajeren bayanin nawa:

  1. Inyamurai na samun tsangwama a jahar Legas tun bayan zaɓen shugaban ƙasa na bana da aka yi ranar 25 ga Fabrairu, 2023, amma duk da tsangwamar ba ta kai ga rasa rayuka ba, sun fara gagarumin shiri na mai da kasuwancinsu Kudu maso gabas wato yankunansu.
  2. A duk yankunan Kudu idan ‘yan Arewa suka samu matsalar tsaro wanda kan janyo asarar rayuka da ɗimbin dukiya sai dai su bar mu da sallallami da ife-ife, amma ba sa iya yin wani babban yunquri na sauya akalar kasuwancinsu zuwa yankinsu, iyaka su jira rikici ya lafa, mai rai ya sake komawa.
  3. A gefe guda abinda muka hango na kafewarmu kan a miqa wa Kudu mulki don ceto Arewa daga rikicin ƙabilanci daga kudu wanda kan laƙume dukiyar ‘ya’yanta da rayukansu, tun ba a je ko ina ba ma hasashen ya fara tabbata, domin da wannan rikicin da ke faruwa tsakanin yarbawa da inyamurai har tuni Inyamuran suka fara nema wa kansu mafita, idan da a ce ɗan Arewa ne zai karɓi mulki a hannun ɗan Arewa a ranar 29 da watan mayu, to da dukansu biyun da xan Arewa suke faɗa a yanzu, kuma da matsalar ma ta fi hakan domin ɗan Arewan da zai karvi mulkin ba zai iya kare rayukan dubban ‘yan Arewan da za su jikkata ba, kamar yadda su ma ‘yan Arewan ba za su iya sauya akalar kasuwancinsu kamar yadda inyamurai suka fara yunƙurin ceton nasu a yanzu ba.

Yanzu dai ga shi mun zama ‘yan kallo daga nesa, wataqil ma wasunmu ba su san me yake faruwa ba don babu nasu a cikin rikicin…

A taqaice dai ya kamata mu san cewa, yunqurin ceton Arewa da ‘yan Arewa ya girmi hayaniyar shafukan sada zumunta da Allah-wadai, dole sai an yi a aikace, sulhu, maslaha, aiki, mafita, sannan hayaniyar soshiyal midiya ta biyo baya.

Sannan sai mun gane cewa don na rasa ɗanuwana a wani yanki na Kudu a bara waccan, bai kamata na fara tunanin ɗaukar fansar da zai sa wasu ma su rasa na su ‘yanuwan ba. Allah Ya sa mu ci gaba da gane karatun.

Rahma Abdulmajid, marubuciya ce, kuma mai sharhi kan al’amurran yau da kullum. Ta rubuto daga Abuja.