Daga FATUHU MUSTAFA
Gaskiya ina murna da wannan mataki da sabon gwamna mai jiran gado ya ɗauka, inda ya yi kashedi ga dukkan waɗanda suka samu filaye a makarantun gwamnati, maƙabartu da masallatai da cewa, gara ma kar su ƙarawa kansu asara, domin yana hawa zai rusa dukkan irin waɗannan gine-gine. To amma fa, bayan dara, akwai wata cacar.
A Kano dai an jima ana ruwa, ƙasa na shanyewa. Dama gwamnonin Kano tun zamanin Rabiu Kwankwaso 1999 – 2023 ta sunnanta wa Kano wannan mummunar aƙida domin dai mun san a zamanin sa aka fara yanka…
- Kano Polytechnic oldside, wurin da ke kallon Audu Bako Secretariat
- WATC Kano, gine-ginen birnin da ke kallon FCE Kano kafin a kai Kabuga, su ma makaranta aka yanka aka yi su.
- Kantinan da aka yi a jikin BUK Old site da ke kallon titin Gwarzo Road. Su ma ya kamata Abba ya tabbatar ba su ƙara ko kwana ɗaya ba.
- Akwai Green Zone da aka kashe su aka sayar da wuraren, akwai biyu na kan Maiduguri Road inda a yanzu gidajen mai ne, da kuma wanda aka yanka sare itatuwan ake gina masallaci, ya kamata a tabbatar an dawo da su yadda suke suma. Akwai guda biyu dake kan State Road daf da gidan Sarki na Nasarawa, inda a yanzu aka bai wa Pizza Hut, su ma ya kamata a tabbatar an rushe su, a dawo mana da bishiyoyinmu.
- Akwai kuma Hotel din Daula, wanda ya taso tun daga Diga sai da ya dangane da titin Murtala Muhammad, Kwankwaso ne ya fara sayar da 70% nasa, Ganduje ya zo ya ƙarasa sauran. Muna kira da Maigirma Sabon Gwamna da ya taimaka a dawo mana da kayanmu.
Akwai dogayen gidajen nan na Sulaiman Crescent inda a zamanin Kwankwaso aka yanka staff Quarters ɗinsu aka sayar, ya kamata su ma a tabbatar an rushe su.
Akwai irin wannan ma a Kundila Zoo Road da ya kamata a tabbatar an rushe duk wani gini da ya haura ƙa’ida ko ya yi wa tsarin karen tsaye.
Ba za mu yadda a ce an ja layi ba. A tabbata an yi abin ba sani ba sabo. Allah ya taimaki sabon gwamna akan wannan kyakkyawar niyya tasa. Fatuhu mustafa marubuci ne kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum.
Ya rubuto daga Abuja.