Tinubu, sarkin nasara!

Daga NASIR I. MAHUTA

Tunda Tinubu ya tsaya takara, ban tava kawowa akwai abinda zI iya hana shi nasara ba.

Tun kafin 2015 na jima da karantar ɗabi’ar Tinubu, a taƙaice, Tinubu na daga cikin mutanen da nake koyi da su wajen samun nasara a duk abin da zan nema.

Tinubu na da wata ɗabi’a da ya sa zai yi wuya ya nemi abu bai samu ba. Allah ne ke ba da nasara, amma akwai ɗabi’a da idan mutum na da ita Allah yana ba shi nasarar a duk abin da ya ke nema. Na san mai karatu zai so ya san ɗabi’ar.

Bari mu leqa cikin ilimin ɗabi’a ta ɗan Adam. Tunubu mutum ne da Allah ya ba shi ɗabi’a irin ta mikiya. Ita ko mikiya sarki ce a cikin tsuntsaye kamar yadda zaki ke sarki a cikin dabbobi. Da zarar ka ji an ce Sarki, to ka san ba a sarki a banza, shi ya sa Allah ya hore ma mikiya baiwar da ta bambanta da sauran tsuntsaye. Da yake maganar Tinubu muke ba maganar mikiya ba, bari na yi maka bayanin mai ya sa na ce Tinubu na da ɗabi’a irin ta mikiya.

Idan mikiya ta hango abin farauta, ba ta tashi zuwa ga abin har sai ta lissafa abubuwa kamar haka:

-Lafiyar abin: Sanin lafiyar abin da za ta farauta shi ne zai nuna mata cewa idan ta farauci abin za ta cinye shi hankali kwanci ba tare da ya haifar mata da illa ba.

-Nisan da ke tsakanin ta da abin: sanin nisan ne zai iya tabbatar mata da idan ta tashi za ta iya samun nasarar kai wa ga abin kafin ya gudu.

Abin da ke kewaye da abin: sanin abin da ke kewaye da abin ne zai nuna mata; ƙarfin da ta ke buƙata, saurin da ta ke buƙata, da yanayin saukar da za ta yi wa abin domin samun nasara.

Duk wannan lissafin mikiya na yi ne kafin ta tashi ta iske abin da ta ke son farauta, kamar haka Tinubu yake. Ɗan siyasa ne da ke lissafin nisan da ke tsakaninsa da kujerar da ya ke nema tun kafin ya nemi kujerar. Yayin lissafin kuma yana cire son da yake yi wa kujerar a gefe sai ya yi amfani da qwaqwalwa wajen gane zai iya kai wa ga kujerar ko ba zai iya kai wa ba. Kuma ko da ya ga zai iya kai wa ga kujerar, ba ya nema sai ya fahimci waɗanda ke zagaye da kujerar da ƙalubalen da zai fuskanta a wajensu. Da zarar ka ji ya nema ɗin, to duk wanda zai ba shi ciwon kai ya sani, kuma ya tanadi yadda zai yi nasara komai yawan ƙalubalen da zai fuskanta. Wannan ne dalilin da ya sa Tinubu bai taba fita zaɓe bai nasara ba. Wannan kuma shi ne abin da ma fi yawan ‘yan Siyasa suka rasa.

Domin samun nasara a yau, Tinubu na iya ɗaukar shekaru yana tsara yadda zai samu nasarar tare da tanadar mafita ga duk ƙalubalen da zai fuskanta. Shi ya sa lokacin da na ji Tinubu zai fito zaɓen fidda gwani, na faɗa wa abokina Rabiu Auwal Kwankwaso kawai cewa ya zura ido ya gani Tinubu zai lashe zaɓen nan.

Abokina ya ce bisa alamu jiga-jigan Jam’iyyar APC ba sa tare da shi kuma fadar shugaban ƙasa ma haka. Na ce masa duk da haka ya jira ya gani. Sai ga shi a daren aka ayyana Tunubu a matsayin wanda ya yi nasara.

To Malam, ka ji tsoron karawa da mutumin da tsananin son da ya ke wa abin ba ya ke nema ba ya sanya shi zumuɗi da gaggawar neman abin. Sannan ƙarfin da yake da shi ba ya zuga shi wajen ganin zai samu abin cikin sauƙi.

Kafin karawa da Tinubu, ka sani za ka kara da mutumin da ya shirya samun nasara tun shekaru goma kafin ka fara son abin.

Ka sani za ka kara da mutumin da ya san lokacin da zai iya samun abin, kuma ya ke iya haƙurin jiran lokacin da idan ya nema zai samu.

Ka sani za ka kara da mutumin da ya gama gane duk wani motsinka sannan ya san ƙoƙarinka kuma ya auna cewa zai yi galaba a kanka kafin ya nemi abin da kake nema.

Batu na gaskiya, a cire batu na son rai, a ‘yan siyasar Nijeriya zai yi wuya ka samu wanda ya fi Tinubu tsananin hikima da basira. Tabbas tsoho ne, amma ƙwaƙwalwarsa girmanta abin mamaki ne. Domin ko a ‘yan siyasar Arewa babu ɗan siyasarsa da lissafinsa ya nuna masa cewa idan aka yi Muslim-muslim za a yi nasara sai Tinubu. Tun a 2015 ya ba wa Buhari shawarar ya zama mataimakinsa ayi Muslim-muslim Ticket amma jiga-jigan APC suka ce idan aka yi haka ba za a yi nasara ba. Shi kuma ya yi imani za a yi nasara, kuma ya tsara yadda za a samu nasara sannan yanzun ya aiwatar ga shi kuma ya samu nasarar.

A halin yanzu, ‘yan siyasar Nijeriya Tinubu ya koyar da su darasin da ba su tava ganowa ba, cewa Musulmi idan ya ɗauki Musulmi Mataimaki to za a ci zaɓe da yardar Allah. Wannan darasin kuma zai canja siyasar Nijeriya gaba ɗaya.