Akwai fahimtar juna tsakaninmu da ƙabilun Jihar Legas – Aliyu Zain

Spread the love

Daga BUSHIRA NAKURA

Blueprint MANHAJA a wannan makon ta samu nasarar tattaunawa da wani matashin ɗan kasuwa, ɗan asalin Jihar Kano, amma mazaunin Jihar Legas da ke gudanar da harkokin kasuwancinsa a jihar ta Legas tsawon shekaru mai suna Aliyu Zainal Abideen. A hirarsa da ya yi da Wakiliyarmu, BUSHIRA NAKURA, ɗan kasuwar ya bayyana yadda Hausawa mazauna Jihar Legas ke da kyakkyawar fahimtar juna tsakaninsu da sauran ƙabilu a jihar. Ya kuma bayyana wasu bambance-bambance da ke akwai ta fuskar tsadar rayuwa da al’adu tsakanin al’ummar Jihar Legas da kuma na Arewcin Nijeriya musamman Jihar Kano, inda ya fito.

Ga dai yadda hirar tasu ta kasance:

MANHAJA: Assalamu alaikum warahamatullah wa barakatuhu. Mai karatu zai ji daɗi idan ka faɗa mana cikakken sunanka da sunan da aka fi saninka da shi. Sannan da tarihinka a taƙaice?

ZAINAL ABIDEEN: Amin wa alaikumussalam warahamatullah wa barakatuhu. Sunana Aliyu Zainal Abideen Umar, an fi sani na da Zain. Ni mutumin Kano ne, an haife ni a ƙaramar Hukumar Dala a unguwar Kurnar Asabe. Na yi karatun firamare a filin Durumi Special Primary School Kurna Asabe. Na yi sakandare a GSS Kwakwachi, Fagge a ƙaramar Hukumar Fagge. Daga nan karatuna ya tsaya.

Ka na yin sana’a ne ko aikin gwamnati?

Ni ba na aikin gwamnati, kasuwanci nake yi. Na fara koyon aikin ‘penal beater’ a ƙofar Ruwa a wajen Oga Taye tsawon shekara 3. Sakamakon rasuwar mahaifinmu Mamana ta tafi da ni Legas bikin ƙaninta inda ta barni can ta dawo Kano, daga nan muka fara sana’ar siyar bushasshen barkono da albasa.

A 2018 gwamnatin Legas ta wancan lokacin ta rushe kasuwarmu ta Ille-epo Oke-odo Market saboda za ta sabuntata bayan rusheta ne muka koma Jihar Ogun a filin wani bawan Allah muka ci gaba da harkokinmu na yau da kullum inda muke harkokin waya.

Ka na da iyali ne? 

Ina da aure; ‘ya’yana biyar, huɗu mata; ɗaya namiji.

Yaya bambancin zaman Legas da Kano yake ta fannin tsadar rayuwa?

Yanayin zaman Legas da Kano zancen gaskiya tsadar rayuwa ta fi yawa a Legas sai yadda nake ganin kuma kamar yawan mu’amala da kuɗin ya fi yawa a nan, shi ya sa da an samu an kashe a taƙaice dai abubuwa sun fi sauƙi a Kano fiye da Legas sosai ma, akwai abinda a nan ‘yan kasuwar Arewarmu suke siya su kai Arewa amma ba sa cin buri a kansa kamar a nan Legos, sai ki ga ya fi sauƙi a Kanon, saboda komai ‘billing’ ne.

Ka na sha’awar dawowa Kano da zama?

Gaskiya Ina da sha’awar dawowa Kano da kasuwancina, amma sai a hankali saboda Legas ba a ci mata alwashi ka ce kai idan ka tafi ba za ka dawo ba, amma ana wasu ‘yan tanade-tanade kafin lokacin komawa in Allah ya yi.

Ya ya rayuwar Legas take?

Rayuwar Legas da daɗi ba daɗi, saboda sai ka daure saboda za ka ga saɓanin al’ada musamman in kai ɗan Arewa ne. Idan kai mai yawo ne a cikin gari za ka ga abubuwan mamaki daban-daban rashin tausayi, ko-in-kula, ga in wani abu ya faru da mutum mutane na gani za su yi fuska. Shi ya sa duk inda za ka je yawo in son samu ne ka gaya wa ɗan uwanka za ka je waje kaza saboda mutane na ɓata sosai.

Daga ina ake kawo muku barkono?

Yanzu ba na harkar borkono sai harkar wayoyi da accessories

Shin ana gudanar da fannin al’adunmu na gargajiya a Legas?

Ana gudanarwa a wasu lokutan kamar lokacin bikin sallah ko biki

Yaya mu’amala take tsakanin Hausawanmu da ƙabilu?

Muna mu’amala mai kyau saboda akwai fahimtar juna musamman ga waɗanda suka fahimci yarensu.

Matarka a nan ku ka haɗu ko Kano ka zo ka yi aure ka kai ta can?

Matata a Legas muka haɗu, da ma dai ‘yar uwata ce kuma a nan aka ɗaura aurenmu da ita, amma lokacin tana Kano. A Kano muka fara tarewa, daga bisani muka dawo nan da zama.

Wane abu ne na farin ciki wanda ba za ka taɓa mantawa da shi ba?

Abin farin cikin da ba zan taɓa mantawa da shi ba shi ne samun ƙaruwar haihuwar ɗa namji da Allah ya azurtani da shi, Ina yi wa Allah godiya. 

Wane abu ne na baƙin ciki wanda ba za ka taɓa mantawa da shi ba?

Mutuwar mahaifinmu! Haƙiƙa wannan na shiga tashin hankali matuƙa a rasuwarsa, kowa yasan cewar uba shi ne bangon da dukkan iyalai ke jingina jikinsa, Allah ya jiƙan babanmu.

Mene ne yake baka tsoro a rayuwa?

Butulci, wanda ka taimakawa ya dawo shine mai cin dunduniyarka, wannan abun na bani tsoro sosai.

Me ka fi so a yi ma kyauta da shi?

Na fi son a yi min kyauta da kuɗi ina matuƙar jin daɗin hakan.

Wane abu ne yake saurin saka jin haushi?

Munafurci, idan aka min munafurci yanzun nan raina zai ɓaci, zuciyata za ta dugunzuma.

Wane kalar abinci da abin sha ka fi so?

Ina son cin shinkafa da wake, abin sha kuma Pepsi.

Yanayin gari wanne ka fi so damina, sanyi ko zafi?

Na fi son yanayin damina.

Mene ne burinka wanda kake son cikawa?

Burina shi ne Allah ya yi min arzikin da zan ringa taimaka wa al’umma

Mene ne kake so ga mutane?

Ina son mutane su haɗe kawunansu su ajiye bambance-bambancen addini da ƙabilanci a tafi tare a tsira tare.

Su waye gwanayenka a duniya?

Gwanaye na Injiniya Dr Rabiu Musa Kwankwaso, His Eɗcellency Engr. Abba kabir Yusuf, Malam Nasiru El-rufai da Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Wacce nasiha za ka yi wa matasa musamman cima-zaune wanda ba su son neman na kansu? 

Nasiha ga matasanmu su nemi abin yi ko yaya yake, a sannu a sannu za su je inda suke fatan domin babu yanayi mai ɗorewa.

Ko ka na da wanda za ka gaisar?

Ina gaishe da abokina Musa Noma ɗan Rimi, Rijiyar Lemo.

Mene ne fatanka ga jaridar Blueprint Manhaja?

Allah ya ɗaukaka gidan jaridar, ya ƙara bai wa ma’aikatansu ƙwazo da aiki a kan gaskiya da riƙon amana.

By ukarofi