Alƙali Nyako ta tsame hannu a shari’ar Nnamdi Kanu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mai Shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ta cire kanta a shari’ar shugaba ƴan ƙabilar Igbo (IPOB), Nnamdi Kanu da ke tsare.

Hakan na zuwa ne bayan Kanu ya nemi Alƙalin ta janye daga shari’ar tasa.

Kanu ya bayyana hakan ne a ranar Talata a lokacin tsaka da ake shari’ar wanda gwamnatin tarayya ke tuhumar sa da laifuka bakwai da ke da alaƙa da ta’addanci.

A lokacin da lauyan Kanu, Mista Alloy Ajimakor ke ƙoƙarin neman kotun ta ɗage shari’ar kasancewar ba a bai wa Kanu damar shirya kare kansa ba, sai Kanu ya umarce shi da ya zauna.

Kanu ya cigaba da cewa, ba shi da aminci da kotun wajen yi masa adalci, don haka ya nemi Alƙalin ta fita daga shari’ar tunda ba za ta bi umarnin kotun ƙoli ba.

Babban lauyan Nijeriya, Adegboyega Awomolo (SAN) shi ke kula da ƙara, inda ya buƙaci kotun ta cigaba da hukuncin sauron shari’ar, amma daga nan sai Alƙali Nyako ta yanke hukunci cire hannunta a cikin shari’ar.

By Babaji