
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ce Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu da Shugaba Bola Tinubu sun san akwai zargin ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle na cewa ya na da hannu acikin ayyukan ta’addanci a jihar.
Gwamnan ya ce, ya sanar da NSA da Shugaba Tinubu game da batun tare da gabatar musu da wasu hujjoji.
Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan Matawalle, wanda tsohon gwamnan jihar ne ya musa batun zargin cewa ya na da alaƙa da ƴan bindiga a jihar.
Cikin wata hira da aka yi da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce Matawalle ƙarya ya ke yi kuma nan ba da jimawa ba za su fitar da hujjojin da ke tabbatar da zargin da ke kansa wa duniya.
Saidai, a lokacin da ake hira da Matawalle a gidan telebijin na ‘Channels, ya ƙalubalanci Gwamna Lawal da Janar Ali Gusau kan su rantse da Al-Ƙur’ani cewa ba su da hannu acikin ayyukan ta’addanci da ke addabar jihar da ma Arewa-maso-Yamma baki ɗaya.
Matawalle ya ce, ba amfani a a jingina masa ɗaukar nauyin ƴan bindiga kasancewar shi ya buƙaci tattaunawa da su a yunƙurinsa na dakatar da kashe-kashe wanda wasu gwamnoni ma sun goyi bayan hakan.
Kawo yanzu ba a kai ga sanin ko Ribaɗu ya fara gudanar da bincike game da batun zargin da ake yi wa ministan ba kasancewar ba a samu amsa game da bayanin hakan ba.
