
Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Dokokin Kogi ta yi kira da a tsige shugaban Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC), Ola Olukoyede kan nuna rashin ƙwarewa game da batun rashawa da ake tuhumar tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello a kai.
An gabatar da hukuncin ne a ranar Litinin a yayin zaman majalisar, a Lokoja babban birnin birnin jihar inda ƴan majalisar suka bayyana samamen da jami’an EFCC suka kai masauƙin gwamnatin jihar da ke Abuja a matsayin cin-fuska ga Gwamnan jihar, Usman Ododo da al’ummar jihar.
Hakan na zuwa ne bayan wani kira na gaggawa da Hon. Akus Lawal da ke wakiltar mazaɓar Ankpa 1 da takwaransa Jakob Olawaunmi daga mazaɓar Ijumu na a sauke Olukoyede daga muƙaminsa suka yi.
Majalisar, baya ga yin nazari game da kai samamen da jami’an EFCC suka yi a ranakun 17 ga watan Afrilu da 18 ga watan Satumba da ayyana su a matsayin yunƙurin kisa akan rayukan tsohon gwamnan da gwamna mai-ci a yanzu.
Akan haka ne ƴan majalisar suka ce EFCC ta sauka daga tsarin aikinta na yaƙi da rashawa saboda shugabanta ya nuna gazawa don haka suka yanke shawarar neman Shugaba Tinubu ya sauya Olukoyede daga muƙaminsa da wani wanda zai iya aiki da doka.
Jaridar ‘Intel Region’ ta ruwaito yadda aka yi ɗauki-ba-daɗi tsakanin jami’an EFCC da jami’an tsaron Gwamna Ododo da Yahaya Bello a masauƙin gwamnatin jihar a makon da ya gabata a Abuja.
A safiyar ranar ne, Bello tare da Ododo suka je hedikwatar EFCC don miƙa kansa kan zargin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta masa na almundahanar kuɗi da adadinsa ya kai Naira biliyan 80.2.
