
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Shari’a Mohammed Nasir Yunusa na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ya rasu.
An ruwaito cewa, alƙalin ya rasu ne a ɗakinsa na kwana bayan ya yanki jiki ya faɗi a daren ranar Alhamis wayewar Juma’a, lamarin da ya sa aka gaggauta garzayawa da shi asibiti inda a nan aka tabbatar da rasuwarsa.
Rahotanni daga Babbar Kotun Tarayya a Abuja sun tabbatar da faruwar al’amarin a yau Asabar. Sun ce tuni aka masa jana’iza a ranar Juma’a.
Ita ma Daraktar yaɗa labaran Babbar Kotun, Catherine Oby Christopher, ta tabbatar da faruwar al’amarin, inda ta ce Mai Shari’a Yunusa ya rasu ne a Cibiyar Lafiya ta Jihar Kano.
Gabanin rasuwarsa, mai shari’ar ya jagoranci hukuncin manyan shari’o’i da suka danganci siyasa a Nijeriya.
