Tinubu ya lallasa Stanley Osifo a zaɓen fidda gwanin APC a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Ɗan takarar neman kujerar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya samu gagarumar nasara a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa da aka gudanar a jihar Gombe bayan da ya kwashi ƙuri’u 450,517.

Tinubu ya doke abokin takararsa guda daya, Stanley Osifo, wanda bai samu ko kuri’a daya ba a sakamakon da aka tattara daga faɗin ƙananan hukumomin jihar 11.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen a cibiyar tattara ƙuri’u ta jihar, gwamnan Gombe kuma jami’in tattara sakamakon zaɓen, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce an gudanar da zaben cikin lumana tare da bin ƙa’idojin jam’iyyar APC.

Ya bayyana cewa za a aika da sakamakon zuwa hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa da ke Abuja domin tattarawa da sanar da sakamakon ƙarshe na ƙasa baki ɗaya.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce jihar Gombe na da jimillar masu rajistar zaɓe 550,516, yana mai bayyana nasarar Tinubu a matsayin wata alama ta karfin APC da kuma irin goyon bayan da yake samu daga al’ummar jihar.

Ya yaba wa shugabannin jam’iyya, wakilai da magoya bayan APC bisa yadda suka gudanar da zaɓen cikin zaman lafiya da nuna biyayya ga tsarin dimokuraɗiyya.

By ukarofi