Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya rasuwa a Yobe

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu

Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan; Hajiya Halima (Dada) rasuwa a mahaifarsa dake garin Gashuwa, shalkwatar ƙaramar hukumar Bade a jihar Yobe.

Yayin da yake sanar da rasuwar, Malam Yahaya Mato, a madadin iyalai da ‘yan uwa, ya bayyana cewa Allah ya yi wa Hajiya Dada; ‘yar kimanin shekaru 90 a duniya rasuwa a Unguwar Katuzu dake cikin garin Gashuwa.

Haka zalika, sanarwar ta bayyana cewa za a yi jana’izar marigayiyar ne gobe Lahadi, 15 ga watan Oktoban 2023, da misalin ƙarfe 11:00 na rana a masallacin ƙofar Fadar Mai Martaba Sarki Bade dake cikin garin na Gashuwa, idan Allah ya kai mu.

Ubangiji Allah Ya jikanta da rahama kuma ya yafe mata kurakuranta, Ya sa Aljannatul Fiddausi ce makomarta, amin.

By Editor