Al’umma na da rawar da za su taka wajen daƙile ta’addanci – Buhari

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce al’ummomin da ke samun goyon bayan gwamnatoci suna da rawar da za su iya takawa wajen daƙile barazanar ‘yan ta’adda.

Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya aike da shi domin nuna damuwarsa game da harin ta’addancin da aka kai Yobe wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.

A saƙon da mai taimaka masa Malam Garba Shehu ya aike wa Gwamna Mai Mala Buni na Yobe, Buhari ya jajentawa majalisar sarakunan jihar da ɗaukacin al’ummar jihar.

Tsohon shugaban ƙasar ya yi addu’a ga waɗanda aka kashe kuma ya yi kira da a mayar da martani ga waɗanda suka aikata “mummunan ayyukan.”

Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun hallaka mutane da dama, suka ƙona gidaje da kantuna tare da wawushe kayayyaki a ƙauyen Mafa da ke ƙaramar Hukumar Taruwa ta Jihar Yobe.

Mayaƙa sama da 50 ɗauke da muggan makamai a kan babura ne suka far wa ƙauyen a yammacin ranar Lahadi.

By ukarofi