RTEAN ta rushe shugabannin reshen Jihar Oyo

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Majalisar Zartaswa ta ƙungiyar Masu Motocin Sufuri ta Nijeriya ta yanke shawarar rusa tsarin shugabannin ƙungiyar reshen jihar Oyo.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Abuja mai ɗauke da sa hannun shugaban RTEAN na ƙasa Alhaji Musa Muhammed Maitakobi da babban sakataren ƙungiyar na ƙasa Comr. Yusuf Ibrahim Adeniyi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bayan shawarwarin da aka cimma a taron majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) da aka gudanar a ranar 29 ga watan Agusta, 2024, a hedikwatar hukumar ta ƙasa, muna so mu isar muku da rusa ƙungiyar RTEAN ta jihar Oyo nan take, bisa doka tare da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki a Sashe na 9: d (ii).

“Wannan matakin ya faru ne sakamakon rashin aiki da shugabannin zartaswa da kuma rashin halartar tarukan ƙungiyar sama da watanni 6 ba tare da wani dalili ba.

“A halin da ake ciki kuma, za a kafa wani kwamiti da zai gudanar da al’amuran jihar har zuwa lokacin da za a zaɓi sabbin shugabannin zartarwa kamar yadda kundin tsarin mulki ya buƙata.

“Ku ƙara lura cewa duk shugabannin zartarwa na jihar nan an rusa su daidai da dokar sashi na 9: (b) na kundin tsarin mulkin ƙungiyar. Na gode da fahimtar ku game da wannan.”

By ukarofi