Al’ummar Katsina sun yi sulhu da Ado Aleru da wasu manyan ɓarayin daji

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu al’ummar Katsina sun yi sulhu da wasu shugabannin ‘yan bindiga da suka addabe su.

Al’ummar garin Bicci da ke yankin ƙaramar hukumar Ɗanmusa sun zauna tare da Ado Aleru da sauran wasu shugabannin ‘yan bindigan aƙalla 10, kamar yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina Dakta Nasiru Mu’azu ya shaida wa manema labarai.

“An zauna da Ado Aleru da Kamilu Buzaru da Dogo Nahali da Wada Jargaba da Ɗahiru Buzu haka ma da Nagoggo,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, a ɓangaren al’umma akwai limamai da ‘yan kasuwa da shugaban ƙaramar hukumar Ɗanmusa.

A cewar kwamishinan ‘yan bindingar ne suka nemi a zauna a yi sulhu don haka ne aka hadu aka tattauna domin tabbatar da zaman lafiyar.

Gwamnatin Jihar Katsina ta sha nanata cewa baza ta yi sulhu da ‘yan bindingar ba, sulhun ne dai duk da cewa gwamnatin Katsina ta sha nanata cewa ba za tayi sulhu da ‘yan bindingan ba amma kwamishinan tsaron Nasiru Muazu ya ce buƙata ce daga ɓangaren ‘yan bindigar don haka gwamnati ta ba su dama.

Ya ce ‘yan bindigan sun bayar da tabbacin ajiye makamansu tare da sako wasu mutane da suka yi garkuwa da su.

Baya dai an yi irin wannan zama da wasu shugabannin ‘yan bindiga da suka addabi yankunan ƙananan hukumomin Jibia da Batsari, inda aka samu sauƙin hare-haren.

By ukarofi