Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnoni daga yankin Arewa maso gabashin Nijeriya sun nuna matuƙar damuwarsu dangane da matsalar ambaliyar ruwa da kuma matsalar ƙarancin abinci, inda suka buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kawo ɗauki domin daƙile bala’in tare da kawo ayyukan jinƙai da kuma da ababen more rayuwa.
Gwamnonin a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF), sun yi wannan kira ne a taronsu na 12 da suka gudanar a Jalingo, jihar Taraba, a ranar Asabar. Taron ya ƙunshi gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba, da Yobe.
A cikin wata sanarwa da gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya karanta, shugabannin sun yi la’akari da hasashen da wasu sahihan hukumomin duba yanayi suka yi na hasashen ambaliyar ruwa a yankin.
Sun jaddada buƙatar ɗaukar matakan da suka dace, da wayar da kan al’ummomin da ke kusa da filayen ambaliyar ruwa, da sake gina kayayyakin more rayuwa cikin gaggawa.
“Majalisar ta yi la’akari da hasashen da hukumomi masu sahihanci suka yi kan haɗarin yanayi da kuma bala’in ambaliyan da ke shirin afkuwa a yankin, don haka ya buƙaci a ɗauki matakan da suka dace wajen tunkarar ambaliyar da kuma wayar da kan mazauna yankunan da ke gabar ruwan.
Ta kuma buƙaci goyon baya daga Gwamnatin Tarayya da Hukumar NEDC don sake gina ababen more rayuwa da suka lalace, musamman gadoji da ambaliyar ruwa ta shafa,” inji sanarwar.
Gwamnonin sun ƙara nuna damuwarsu kan tsadar kayan amfanin gona kamar taki, irin shuka da kayayyakin amfanin gona na zamani, inda suka yi gargaɗin cewa hakan na iya yin illa ga ayyukan noma da kuma haifar da ƙarancin abinci a yankin a shekara mai zuwa.
Domin tinkarar wannan rikici, sun yi kira da a ƙara ba manoma tallafi, da bayar da tallafi mai ƙarfi ga noman rani, da kuma shirya tsaf don noman rani.
“ƙungiyar ta nuna rashin amincewa da tsadar kayan amfanin gona, wanda zai iya haifar da mummunan sakamako ga amfanin gona a shekara mai zuwa. Don kaucewa matsalolin abinci da ke gabatowa, ya buƙaci karin tallafi ga manoma da kuma shirye-shiryen noman rani,” inji su.
Yayin da suka amince da “nasara mai kyau” a ci gaba da ayyukan soji na yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabas, gwamnonin sun koka da cewa har yanzu yankin na fama da ƙalubalen jinƙai da samar da ababen more rayuwa.
Sun buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da hukumomin tarayya da abin ya shafa da su wuce hanyoyin tafiyar da al’amura, inda suka jaddada cewa ilimi, kiwon lafiya, ƙarfafawa matasa, koyon fasahar ƙere-ƙere, da samar da ababen more rayuwa su ne jigon daƙile rashin tsaro a cikin dogon lokaci.
Gwamna Zulum ya jaddada cewa dole ne a magance batutuwan da suka haɗa da taɓarɓerewar matasa, rashin aikin yi, rashin hanyoyin sadarwa, da rashin isassun shirye-shiryen rage radadin talauci idan ana son ɗorewar nasarorin da aka samu a kan ‘yan tada ƙayar baya.
Baya ga magance matsalolin tsaro da muhalli, gwamnonin sun ƙuduri aniyar karfafa dunƙulewar yankin ta hanyar kasuwanci, makamashi da haɗin gwiwar tattalin arziki.
Muhimman audurori sun haɗa da: gudanar da bikin baje kolin kasuwanci na arewa maso gabas a Maiduguri, jihar Borno, a watan Disamba na shekarar 2025, da samar da wani haɗaɗɗen tsarin samar da wutar lantarki a yankin domin samar da makamashi mai amfani da hasken rana da kuma rage talaucin makamashi da kuma bin matakan haɗin gwiwa kan tsaro, samar da ababen more rayuwa, da bunƙasar tattalin arziki.
Gwamnonin sun kuma yaba da irin “haɗin gwiwa da ba a taba ganin irinsa ba” a tsakanin ƙasashe mambobin ƙungiyar tare da sake dagewa wajen bin dabarun haɗin gwiwa don ci gaban yankin. An shirya taron NEGF na gaba a Maiduguri tsakanin 12 zuwa 14 ga Disamba, 2025.
Gargaɗin na zuwa ne a kan yadda matsalar ambaliyar ruwa ke kara ƙamari a Nijeriya, wanda a shekarar 2022 kaɗai ya raba sama da mutane miliyan 1.4 da kuma lalata dubban kadada na gonaki a faɗin ƙasar.
Yankin Arewa maso Gabas, wanda tuni ya raunana sama da shekaru goma na tashe-tashen hankula da rikice-rikice, ya kasance ɗaya daga cikin yankuna masu rauni.
