Amfanin ayaba ga lafiyar jiki da fata

Daga AISHA ASAS

Duk wani abu da Allah Ya samar da shi a doron ƙasa na daga ci ko sha yana da matuƙar muhimmanci ga rayuwar wanda aka yi shi domin su, wato ɗan Adam. Sannan a cikin duk wani tsiro akwai alfanun da yake tare da shi ga jikin ɗan Adam, sannan a cikin sa za a iya samun waraka daga wata cuta.

A yau shafin kwalliya na jaridar Manhaja zai ɗauko ɗaya daga cikin ire-iren ababen da Allah Ya ni’imta mu da su, wato ayaba. Ayaba ɗaya daga cikin kayan marmari ce da ta ke da sauƙin samu, kasancewar za a iya samun ta da ƙarancin kuɗi, sai dai tana daga cikin layin farko na kayan ci da ke da matuqar tasiri a lafiyar gangar jiki, ciki kuwa har da fata.

Mai karatu zai iya amincewa da zancena tun ban yi nisaba, idan ya yi duba da a cikin littafi mai tsarki ma Allah ya yi wa bayinsa salihai alƙawari da ita a cikin aljanna, za ka samu wannan a cikin suratul waqi’a, inda Yake cewa, bismillahi Rahmanin Rahim, “…..da wata ayaba mai yawan ‘ya’ya’.” (a duba aya ta 27-30).

Da wannan za ka iya amincewa ita karan kanta ayaba ni’ima ce ga ɗan Adam, domin ba wani abu da za a iya tarrarwa a aljanna face ababen jin daɗi, kenan ayaba na ɗaya daga cikin su.

Idan mun juya ɓangaren sahihin likitanci, wato likitancin Musulunci, sun bayyana mana tana da matuƙar amfani ga jikin mutum, kamar yadda sakamakon wani bincike da suka yi a shekarar 1991 ya tabbatar.

A ɓangaren da muka fi mayar da hankali kuwa, wato kalaman bature, su ma sun tabbatar da akwai sinadari mai ƙarawa jiki ƙarfi a cikin ayaba, wato ‘carbohydrate’.

Kada in ja ku da nisa, domin zan so mu kawo wasu daga cikin ababen da ayaba ta ke yi a jiki da kuma magunguna.

Mai matsalar hawan jini, idan jinin ya yi sama, yawan cin ayaba na saukar da shi. Haka ma an tabbatar tana da matuqar tasiri wurin warkar da cutar gyambon ciki, wato ulcer. Ana cin ta ne a kullum kafin a cin abinci. Su ma yara tana taimaka wa ƙwaƙwalwarsu wurin nazari da hazaƙar.

A wani ɓangare kuwa, ana amfani da kowanne sashe na ayaba wurin haɗa wani magani da zai iya warkar da wata cuta. Idan ki ka dafa iccen ayaba, ya dahu sosai, ana shan ruwan don samun sauƙi daga cutar ƙyanda, ciwon kai da kuma zazzaɓi. Za a so a sha kofi biyu zuwa uku a rana.

Su ma masu ciwon zuciya, ana so su yawaita cin ayaba, domin tana taikamawa matuƙa a tafiyar samun lafiyar zuciyar.