Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shahararren mai fafutukar kare muradun Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana cewa har yanzu yana jiran amincewar Gwamnatin Tarayya ta Nijeriya domin fara aikin rundunar tsaro da ya kafa mai suna “Iru Ekun Security Network”, wacce aka tsara domin taimakawa wajen fatattakar masu aikata laifuka daga dazukan Kudu maso Yamma.
Igboho ya kuma bayyana shirinsa na bin dokar zartarwa da Gwamnatin Jihar Oyo, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde, ta fitar, wacce ke tsara yadda ƙungiyoyin tsaro masu zaman kansu za su rika gudanar da ayyukansu a jihar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Ibadan, ya ce dukkan takardu da sharuddan da ake buƙata domin amincewa da rundunar Iru Ekun Security Network an riga an miƙa su ga Gwamnatin Tarayya, kuma yanzu saura jiran sahalewar hukuma.
Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Seyi Makinde ya rattaba hannu kan Dokar Zartarwa Mai Lamba 001 ta Shekarar 2026, wacce ta shafi tsarawa da kula da ƙungiyoyi da cibiyoyin da ke ba da hidimar tsaro da makamantansu a jihar Oyo.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki ya zama wajibi ne domin tabbatar da cewa dukkan ƙungiyoyin sa-kai da masu tsaron al’umma suna aiki cikin tsari, bin doka da oda, tare da tallafawa zaman lafiya da tsaron jama’a.
A nasa ɓangaren, Sunday Igboho ya ce: “Mun miƙa dukkan takardun da ake buƙata domin rajistar rundunar mu ta Iru Ekun Security Network, kuma muna jiran amincewar Gwamnatin Tarayya kawai, wacce muke sa ran za ta fito nan ba da jimawa ba.”
Ya ƙara da cewa, rundunar sa a shirye take ta yi aiki tare da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, Hukumar Tsaro ta DSS, Sojojin Nijeriya, da Hukumar NSCDC domin fatattakar ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu tada zaune tsaye, musamman a yankunan karkara.
Igboho ya kuma yaba wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙoƙarinsa na gyara tsarin tsaro a Kudu maso Yamma da ma sauran sassan ƙasar nan.
Ya ce, mulkin Tinubu na nuna ƙwazo wajen tunkarar matsalolin tsaro, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da al’umma domin kawo ƙarshen rashin zaman lafiya.
Ya ƙara da cewa rashin tsaro na hana ci gaban tattalin arziki musamman a yankunan karkara da ke dogaro da noma, yana mai jaddada cewa zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaban ƙasa.
