Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa janyewar gwamnan jihar Riɓers, Siminalayi Fubara, daga takarar gwamna a 2027 ya yi daidai da yarjejeniyar sulhun da aka cimma domin dawo da zaman lafiya a jihar.
Wike ya bayyana haka ne bayan duba wasu ayyukan more rayuwa a Abuja, inda ya ce tun farko an cimma matsaya cewa za a dakatar da barazanar tsige Fubara, amma shi kuma ba zai nemi wa’adi na biyu ba.
Fubara dai ya janye daga zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, yana mai cewa ya dauki matakin ne domin zaman lafiya, hadin kai da kwanciyar hankali a Riɓers bayan tuntuba da iyalansa da magoya bayansa.
Wike ya ce bai yi mamakin matakin ba, yana mai zargin cewa daukar fom din takara tun farko ya saba da yarjejeniyar sulhun da aka cimma bayan rikicin siyasar jihar.
Haka kuma, ya bayyana ɗan majalisar tarayya, Kingsley Chinda, a matsayin wanda ya dace da kujerar gwamna saboda kwarewarsa a bangaren zartarwa da majalisa.
A gefe guda, kungiyar Riɓers Professionals ta yaba da fitowar Chinda a matsayin dan takarar APC, tana mai cewa yana da kwarewa da nagartar da za su tabbatar da shugabanci mai adalci da hada kan al’umma a jihar Riɓers.
Rikicin siyasar Riɓers dai ya samo asali ne daga sabanin da ke tsakanin Wike da magajinsa Fubara kan iko da tsarin siyasar jihar tun bayan hawan Fubara mulki a shekarar 2023.
