Nijeriya ta soke lamunin Dala biliyan 717 na Bankin Duniya kan lantarki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta Nijeriya ta soke jimillar dala miliyan 717.7 da ba a fitar ba daga wani shirin lamuni na Bankin Duniya, wanda aka tsara domin farfaɗo da sashen wutar lantarki a ƙasar nan.

Rahoton da aka samu ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya ta Nijeriya da Bankin Duniya, sakamakon gazawar cika wasu muhimman sharuɗɗan sauye-sauye da aka shimfiɗa a cikin shirin.

An kuma bayyana cewa an rage wa’adin kammala shirin daga watan Yuni 2027 zuwa Mayu 2026, matakin da ke nuni da dakatar da wani ɓangare na shirin tun kafin lokaci.

Wannan lamuni na dala biliyan 1.52 an ƙirƙira shi ne domin inganta samar da wutar lantarki, ƙarfafa tsarin kuɗi na sashen, da kuma inganta gaskiya da riƙon amana a harkokin wutar lantarki. Duk da cewa an samu wasu ci gaba a matakin farko, amma ɓangaren ƙarin kuɗaɗen ya gamu da matsaloli na jinkiri, raunin aiwatarwa da sauye-sauyen tattalin arziki.

Babbar matsala ta taso ne bayan sassauta tsarin musayar kuɗi a shekarar 2023, wanda ya sa farashin iskar gas da ake amfani da shi wajen samar da wuta ya yi tashin gwauron zabi, yayin da kuɗin wutar lantarki bai samu daidaito ba. Wannan ya janyo giɓin kuɗi tsakanin farashi da kuɗin shiga ya ƙaru sosai, daga kusan Naira biliyan 140 a 2022 zuwa kusan Naira tiriliyan 1.9 a 2024 da 2025.

Bankin Duniya ya bayyana cewa Nijeriya ta gaza gabatar da sahihin tsari na kuɗi da zai iya magance wannan gibin, lamarin da ya sa ci gaba da sakin kuɗin ba zai yiwu ba.

Duk da wasu nasarori da aka samu a baya, kamar rage gibin farashi da inganta dawo da kuɗaɗe, sashen wutar lantarki na ci gaba da fuskantar manyan matsaloli na tsarin rarraba wuta, ƙarancin ƙarfin layukan watsa wuta da kuma rashin daidaiton kuɗi.

Masana na ganin cewa wannan mataki na soke lamunin zai ƙara nuna irin ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta wajen gyara sashen wutar lantarki, musamman a daidai lokacin da farashi ke ƙaruwa, da kuma giɓin manufofi da aiwatarwa ke ƙara bayyana.

By ukarofi