Fasahar zamani na ƙara inganta ƙananan kasuwanci a Afirka – Bankin Duniya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani sabon bincike da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa, tsarin biyan kuɗi na fasahar zamani yana ƙara zama ginshiƙi mai muhimmanci wajen inganci da gudanar da harkokin kasuwanci a Afirka, musamman ga ƙananan da matsakaitan masana’antu (SME).

Rahoton mai taken “Firm Credit Constraints and Electronic Payments: A Global Analysis” ya bayyana cewa amfani da hanyoyin biyan kuɗi na zamani ba wai kawai yana rage ɓata lokaci ba ne, har ma yana ƙara wa ’yan kasuwa damar samun lamuni daga cibiyoyin kuɗi.

Rahoton ya bayyana cewa a yawancin ƙasashen Afirka, galibin mu’amalar kasuwanci har yanzu ana yin ta ne da tsabar kuɗi, lamarin da ke sa yawancin ’yan kasuwa su kasance ‘marasa kwarjini’ a idon bankuna. Wannan kuwa yana hana su samun lamuni duk da cewa kasuwancinsu na tafiya cikin inganci.

A cewar binciken, bankuna a duniya suna dogaro da bayanan shigar kuɗi, tsarin biyan kuɗi da tarihin kasuwanci kafin su amince da bayar da lamuni. Idan waɗannan bayanai ba su samuwa, to mai kasuwanci yana fuskantar matsalar rashin samun kuɗin tallafi.

Binciken da aka yi kan kamfanoni 48,581 a ƙasashe 101 ya nuna cewa kusan kashi 14.78 na kamfanoni ba su da damar samun kuɗin waje kwata-kwata, yayin da kashi 16.23 ke da ƙarancin damar samun lamuni. Jimilla, sama da kashi 30 na kamfanoni masu rajista a duniya ba sa samun isasshen tallafin kuɗi.

Rahoton ya kuma nuna cewa kamfanonin da ke karɓar kuɗi ta hanyar dijital—ta banki, wayar hannu ko kati – sun fi samun damar samun lamuni fiye da waɗanda ke amfani da tsabar kuɗi kaɗai.

Bankin Duniya ya bayyana cewa duk lokacin da aka biya kasuwanci ta hanyar dijital, ana barin sahihin tarihi na mu’amala kamar lokaci, adadin kuɗi da yawan ma’amala. Wannan bayanai suna taimaka wa bankuna wajen tantance ƙarfin kasuwanci.

A cewar rahoton, karɓar kuɗi ta dijital na rage yuwuwar rashin samun lamuni da kashi 3.3, wanda ke daidai da kashi 22 na matsalar da aka gano a binciken.

Rahoton ya jaddada cewa shigar kuɗi, wato payment inflows ya fi muhimmanci fiye da fitar kuɗi, domin yana nuna ainihin ribar kasuwanci wacce bankuna ke dogaro da ita wajen yanke shawarar bayar da bashi.

ƙananan kasuwanci, musamman waɗanda ke da ma’aikata ƙasa da 20, sun fi cin gajiyar wannan tsarin, inda rashin samun lamuni ke raguwa da kusan kashi 4.

A matakin ƙasa, rahoton ya nuna cewa tasirin tsarin biyan kuɗi na dijital ya fi ƙarfi a ƙasashen da ke da ƙarancin kuɗi da kuma ƙarancin tsarin rajistar bashi.

Haka kuma, rahoton ya bayyana cewa Afirka ta haɗa abubuwa biyu masu ƙarfi: ƙarancin bankuna na gargajiya da kuma yawaitar amfani da kuɗin wayar hannu.

Rahoton ƙungiyar GSMA ya nuna cewa a shekarar 2025 kaɗai, an sarrafa sama da dala tiriliyan 1.4 ta hanyar kuɗin wayar hannu a Afirka, tare da ƙaruwa da kashi 27 cikin shekara guda. Afirka kuma na riƙe kashi 52 na asusun kuɗin wayar hannu a duniya.

Kamfanoni na fintech kamar 4G Capital a Gabashin Afirka da Moniepoint a Nijeriya na amfani da wannan bayanan dijital wajen bayar da lamuni ga ƙananan ’yan kasuwa.

Rahoton ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin tsarin biyan kuɗi daban-daban, domin idan bayanai suka rarrabu, bankuna ba sa iya amfani da su yadda ya kamata.

A ƙasashen ƙungiyar Tattalin Arziƙi ta Yammacin Afirka (WAEMU), an tsara ranar 30 ga Yuni 2026 a matsayin wa’adin da dukkan cibiyoyin kuɗi dole su shiga tsarin biyan kuɗi na haɗin gwiwa na lokaci ɗaya (PI-SPI).

Rahoton ya kammala da cewa ƙasashen Afirka na buƙatar manufofi uku: faɗaɗa tsarin biyan kuɗi na haɗin gwiwa, shigar da bayanan mu’amala cikin tsarin bayar da lamuni, da kuma ƙirƙirar dokoki masu kare bayanan ’yan kasuwa.

By ukarofi