Ni na taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Buhari ba Tinubu ba — Amaechi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Ministan Sufuri kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya kalubalanci ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne kaɗai ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a zaɓen 2015.

Amaechi ya bayyana cewa shi ne ya jagoranci mafi yawan yaƙe-yaƙen siyasa da suka bai wa APC nasara a wancan lokaci, ba Tinubu ba.

Yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Tɓ a daren Juma’a, Amaechi ya ce Tinubu, wanda a lokacin yake tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a APC, bai taka rawar da ake bayyana ba wajen tabbatar da nasarar Buhari.

Amaechi, wanda ya taba zama Darakta Janar na yakin neman zaben Buhari har sau biyu, ya ce bai iya mayar da martani ga ikirarin Tinubu a lokacin ba saboda yana cikin majalisar ministocin Buhari kuma yana tsoron rasa mukaminsa.

“Lokacin da nake Minista, Tinubu yana cewa shi ne ya sa Buhari ya zama shugaban ƙasa, amma ban iya magana ba saboda hakan zai iya jawo a kore ni daga aiki,” in ji Amaechi.

Ya ƙara da cewa: “Tinubu bai sa Buhari ya zama shugaban ƙasa ba. Ni ne Darakta Janar na kamfen ɗin, kuma kowa ya san ni ne na yi mafi yawan gwagwarmayar siyasa, ba Tinubu ba.”

Ana tuna cewa kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Tinubu ya sha bayyana cewa shi ne ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da Buhari ya zama shugaban ƙasa a 2015, yana mai cewa “lokacinsa ne” ya jagoranci Nijeriya.

By ukarofi