Martani mabambanta sun biyo bayan neman afuwar Gwamna Aliyu ga Wamakko

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

An samu ra’ayoyi mabambanta daga jama’a bayan Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya nemi afuwar al’ummar jihar tare da durƙusawa a gaban tsohon gwamna kuma jagoran APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, yayin taron tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

A wajen taron da aka gudanar a sakatariyar APC ta jihar, gwamnan ya roƙi al’umma da su yafe masa kan duk wata kura-kurai da ka iya faruwa a cikin shekaru kusan uku na mulkinsa.

“Ba mu yi wa kowa laifi da gangan ba cikin shekaru biyu da watanni 11 da kwanaki 21 na mulkinmu. Ina neman afuwar duk wanda muka ɓata wa rai ba tare da sani ba. A madadina da mataimakina, muna roƙon Allah Ya gafarta mana baki ɗaya,” in ji shi.

Daga nan sai ya juya zuwa ga Sanata Wamakko inda ya ce:

“Mai girma ubangida, a matsayina na ɗanka a siyasa, akwai yiwuwar na yi wasu kura-kurai. A matsayina na Ahmad Aliyu da Ahmadun Alu, ba a matsayin gwamna ba, ina sake neman afuwarka.”

Wannan mataki ya jawo muhawara a jihar Sokoto da ma sauran sassan ƙasar nan, inda mutane da dama suka bayyana mabanbantan fahimta kan lamarin.

Wani mai sharhin siyasa, Dakta Ibrahim Baba Shatambaya, ya bayyana cewa ana iya kallon matakin ta fannoni daban-daban. A cewarsa, hakan na iya kasancewa dabarar siyasa saboda irin tasirin da Wamakko ke da shi a siyasar Sokoto, ko kuma wata alama ta biyayya da girmamawa ga uban gida a siyasa.

“Lokacin da wasu ‘yan siyasa ke watsi da masu gidansu bayan sun samu mulki, wannan mataki na nuna ci gaba da biyayya da mutuntawa,” in ji shi.

Shi ma Alhaji Cika Mairago Sarkin Gishiri na jam’iyyar ADC ya ce neman afuwar gwamnan na da alaƙa da neman goyon bayan siyasa daga Wamakko. Ya ƙara da cewa ADC ta fi dogaro da Allah a dukkan harkokin siyasa.

“Mutane da yawa sun yi imanin cewa ba za ka yi nasara a siyasar Sokoto ba idan ba ka tare da Alu,” inji shi.

Wani ɗan ADC, Naziru Maikulki, ya bayyana matakin a matsayin dabarar neman tausayi daga jama’a kamar yadda aka saba yi a lokacin yaƙin neman zaɓe. Ya ce mutane sun zaɓi Ahmad Aliyu ne saboda sun ɗauke shi a matsayin mutum na gari mai kusanci da talakawa, amma har yanzu yankunan karkara ba su ga cikakken tasirin mulkinsa ba.

Sai dai wani magoyin bayan APC, Abba Abubakar, ya kare gwamnan yana mai cewa matakin ya nuna tawali’u da biyayya.

“Duk wanda ya san siyasar Sokoto ya san gwamnan mutum ne mai mutunci da biyayya. Ban ga wata matsala tsakaninsa da Wamakko ba,” inji shi.

Shi ma Aliyu Ibrahim Layin-Iska ya ce wannan ba sabon abu ba ne, domin Wamakko tamkar uba ne ga siyasar Sokoto kuma dangantakarsu ta ginu ne kan mutuntawa.

A kafafen sada zumunta ma an samu mabambantan martani, inda wasu suka yaba da tawali’un gwamnan yayin da wasu suka ɗauki matakin a matsayin wata dabarar siyasa.

By ukarofi