Amorim ya kafa tarihin samun nasara a wasansa na farko a Manchester United

Spread the love

Amorim ya zama kocin Man United na farko a wasan firimiya a gida da ya ci ƙwallo sama da biyu, karon farko da Man United ta zura 4-0 a bana a gasar.

Manchester United ta doke Everton 4-0 a wasan mako na 13 a gasar Firimiya da suka kara ranar Lahadi a Old Trafford.

Marcus Rashford ne ya fara cin ƙwallo tun kan hutu, na shida da yake da hannu a cin Everton daga karawa ta takwas kenan.

Bayan da suka koma zagaye na biyu Man United ta ƙarasa zura uku a raga ta hannun Joshua Zirkzee, sannan Rashford ya ci na biyu kuma na uku, sai Zirkzee ya kara na huɗu kuma na biyu a wasan.

Wannan shi ne karon farko da sabon koci Ruben Amorim ya ja ragamar Man United a Old Trafford a Firmiya, bayan maye gurbin Erik ten Hag, wanda aka kora cikin watan Oktoba.

Tun kafin nan, Amorim ya fara jan ragamar Man United a Premier da ya je ya tashi 1-1 a gidan Ipswich ranar 24 ga watan Nuwamba.

Haka kuma kocin ya ja ragamar United ta doke Bodo Glimt 3-2 a Europa League a Old Trafford ranar Alhamis 28 ga watan Nuwamba.

Man United tana ta tara a teburin Premier da maki 19, bayan cin wasa biyar da canjaras huɗu aka doke ta karawa huɗu daga fafatawa 13 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

By ukarofi