Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A cikin wani rahoto da ofishin Odita-janar na ƙasa, ya fitar a farkon wannan mako ya nuna yadda Babban Bankin ƙasa, CBN, ya gaza ba da bayanai kuɗaɗen da ke asusun na Nijeriya na ƙetere da suka kai Dala biliyan 40.23 na hada-hadar kuɗi ta shekarar 2021.
Rahoton kuɗin wanda aka fitar a wantan Dimbar 2024, ya uma nuna cewa CBN a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugabanta, Godwin Emefiele, ta karya dokokin gudanar da tsarin ajiyar Dala.
Emefiele yana fuskantar zarge-zarge ne daga hukumar EFCC a babbar kotun tarayya da ke Abuja, kan sama da faɗi da kuɗin al’umma a lokacin shugabancinsa da ya ƙare a watan Yunin 2023.
EFCC ta ce Emefiele ya yi amfani da wasu hanyoyi na ƙarya wajen samun Dala miliyan 6.2. Ana zarginsa da rubuta wasiƙar ƙarya wajen wacce ya yi iƙirarin sakataren gwamnati ne ya rubuta ta a ranar 26 ga watan Janairun 2023 mai (Ref No. SGFF.43/L.01/201) da nufin CBN ta ba da kuɗaɗen don siyo wasu kayayyki bisa umarnin shugaban ƙasa.
Odita na ƙasa, ya bayyana cewa “bankin ya gaza ba da bayanai game da kuɗin da suka kai Dala biliyan 40,230,803,228.80 daga kuɗaɗen ajiya na ƙasar waje.”
Rahoton ya bayyana faruwar hakan a matsayi “rauni da aka samu wajen bin ƙa’idojin gudanarwa na bankin.”
Kuma ƙin biyan waɗannan dokoki sun saɓa da sashe na 15(ɓ) na dokar zuba hannun jari da aka yi wa kwaskwarima ta bankin wacce ta ƙunshi lallai ne bankin na tanada bayanai da takardu na gudanar da kuɗaɗen asusun ajiya na ƙetere saboda tabbatar da gaskiya .
Oditan ya bayyana haɗarin da hakan ke da su ga adana muhimman bayanai na gwamnati da kuma matsayin gaskiya da ka iya cutar da tattalin arziƙin Nijeriya.
Sai dai babban bankin ya ce duk wani mai bukatar ganin bayanin harkokin asusun kuɗin Nijeriya na ƙetare zai iya yin hakan ta hanyar ziyartar shafinsu na Intanet. Haka ma kwamitin kula da harkokin kuɗi na bankin wanda ke zama duk bayan wata biyu, shi ma yakan fitar da bayanai kan waɗancan kuɗaɗe.
Duk wa da wannan martani, ofishin Odita-janar ɗin ya ce wannan bayani bai cika ba wajen gamsar da al’umma batun da ake.
Ofishin Odita-janar ya buƙaci gwamnan CBN da ya bayyana gaban kwamitin kula da asusun majalisun ƙasar nan domin yin cikakken bayani game da rashin wallafa bayanai kan wancan asusu.
Sannan ya buƙaci a ɗau mataki kan bankin kamar yadda yake ƙunshe a dokokin kula da harkokin kuɗin na 2009 bisa zargin laifin almundahana da ke sakin layi na 3129 da ma sauran laifuka da suka shafi kuɗi.
