A ranar Talata, 12 ga Agusta, 2025, ƙasashen Amurka da Chana sun sanar da tsawaita yarjejeniyar dakatar da ƙarin harajin kaya na tsawon kwana casa’in (90), domin daƙile tashin hankali a harkar kasuwanci tsakanin manyan ƙasashen biyu.
Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan kasuwar Amurka ke shirin ƙarfafa ajiyoyin kayansu na bikin ƙarshen shekara, inda tsawaita wannan yarjejeniya zai ba su damar gudanar da ciniki ba tare da tsananin ƙarin kuɗin kaya ba.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da wannan tsawaitawa a shafin sa na Truth Social, inda ya ce, an ɗage ƙarin harajin zuwa ranar 10 ga Nuwamba, 2025.
Haka zalika, ma’aikatar kasuwanci ta Chana ta tabbatar da tsawaita wannan yarjejeniya, tare da jinkirta wasu takunkumi da aka shirya sanya wa kamfanonin Amurka.
A cewar sanarwar Trump, wannan tsawaita na ba da dama ga ‘yan sasantawa su ci gaba da tattaunawa kan batutuwan da suka shafi rashin daidaito a hulɗar kasuwancin da ke tsakaninsu, musamman waɗanda suka shafi tsaron ƙasa da tattalin arziki.
Masana harkokin tattalin arziki sun yi gargaɗin cewa, duk da cewa wannan tsawaita na kawo kwanciyar hankali na ɗan lokaci, har yanzu akwai rashin tabbas a tsakanin kasuwanni, inda sauye-sauyen siyasa na iya kawo koma baya a duk lokacin da aka yi tsammani.
Wannan tsawaitawar ta kawar da barazanar sanya ƙarin haraji mai tsanani da aka shirya fara wa nan take a ranar 12 ga Agusta, wanda zai iya kawo koma baya ga ci gaban tattalin arzikin ƙasashen biyu.
Don haka, kasuwanni sun amshi wannan mataki da murna, inda aka samu ƙaruwar kasuwancin hannayen jari a kasuwannin duniya, musamman a nahiyar Turai da Asiya.
Saidai duk da wannan, masana suna nan a kan gaba wajen lura da yadda abubuwa za su kaya a watannin masu zuwa, musamman yadda wannan yarjejeniya za ta iya tasiri ga kasuwancin duniya baki ɗaya.
