Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills Jr., ya bayyana cewa aƙalla ‘yan Najeriya 201 ne ke cikin sansanonin shige da fice da za a mayar gida daga Amurka, bisa manufofin shige da fice na Shugaba Donald Trump. Daga cikin waɗannan, an riga an tantance mutane 85 don gaggauta korarsu daga ƙasar.
Jakadan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da ministar harkokin waje ta Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, inda ya tabbatar da cewa za a sauke su ne a birnin Legas ba tare da wata matsala ba. Ya ƙara da cewa waɗanda za a fara mayarwa gida su ne waɗanda suka aikata laifuka kuma suke ɗaure a gidajen yari na Amurka. Haka kuma, akwai waɗanda suka karya dokokin shige da fice na ƙasar.
Ministar ta buƙaci da a yi wa ‘yan Najeriya da za a mayar gida cikakkiyar adalci da mutuntawa. Ta bayyana damuwa kan yadda ake ɗaure mutanen da ake korarwa da sarƙa a hannayensu da ƙafafunsu. Ta kuma nemi Amurka ta ba su damar tattara dukiyoyinsu kafin a tura su gida, domin hakan zai rage raɗaɗin da za su fuskanta.
A gefe guda, jakadan Amurka ya yi tsokaci kan tsarin kasuwanci da ciniki tsakanin Amurka da Afrika, musamman dokar African Growth and Opportunity Act (AGOA). Ya ce gwamnatin Trump na da burin mayar da hankali kan haɓaka kasuwanci da tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu. Ministar ta buƙaci Amurka da ta sake duba dakatar da tsarin Drop Box Visa domin rage wa ‘yan Najeriya wahalar samun takardar izinin shiga ƙasar.